Cibiyar Hajjin Nijeriya na shirin ƙarfafa alaƙar aiki da cibiyar bankin Musuluncin Saudiyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Cibiyar Hajji ta Nijeriya (HIN) ta ɗauki muhimmin matakin ƙarfafa haɗakarta ta ƙasashen waje ta hanyar aikin haɗin-gwiwa da Cibiyar Bankin Ci-gaba na Musulmi (IsDBI) a Jeddah da ke ƙasar Saudiyya.

An bayyana haka ne a wata sanarwa da hukumar gudanarwar cibiyar ta fitar a ranar Laraba, 18 ga Nuwamba, 2026, inda Shugaban HIN, Farfesa Nasiru Maiturare wanda ya samu rakiyar Farfesa Wasiu Gabadeen a ziyarar da suka kai wa Darakta-Janar na IsDBI, Dakta Sami Al-Suwailem a ofishinsa domin faɗaɗa haɗin-gwiwa kan binciken haɗaka, horarwar kan ƙwarewa a ayyuka na musamman, inganta lamuran cibiyoyi da salon ƙirƙira wajen gudanar da ayyukan hajji da umara.

A yayin ganawar, IsDBI ta bayyana aniyarta ta bai wa HIN tallafi ta ayyukan haɗakar bincike da yiwuwar ba ta tallafin kuɗi musamman kan nazarin da suka shafi tattalin Hajji da wasu shirye-shirye da suka shafi ibadun biyu, don haka ta faɗaɗa damarmakin karatun ƙwarewa a fannin.

Sannan, akan haka ne IsDBI ta bayar da tallafin ɗaruruwan littafai da wasu wallafe-wallafen masana ga HIN, waɗanda suka taimaka wajen bunƙasa albarkatun ɗakin karatu da binciken cibiyar.

Wannan ya nuna yadda HIN ke ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau kan nazarin ilimin ayyukan hajji da umara a Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani wajen ƙarfafa wa lamuran bincike. Ana sa ran wannan ci-gaba ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ƙwarewa, ingancin aiki da ci-gaba mai ɗorewa a masana’antar harkokin hajji da umara a Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply