Gwamna Raɗɗa ya naɗa Abdul’aziz Salisu a matsayin babban sakatare

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya amince da naɗin ƙwararren ɗan jarida Abdul’aziz Salisu a matsayin babban sakatare a gwamnatin Jihar Katsina.

Wannan naɗin na daga cikin naɗin na gidan talabijin KTTV da ke Katsina inda nan ne ya riƙe muƙamin daraktan kula da harkokin yau da kullum na KTTV.

Abdul’aziz tsohon kuma ƙwararren dan jarida da ya ɗauki tsawon shekaru yana gudanar da aikin jarida kuma ya bada gudunmawa wajen cigaban aikin jarida da faɗakar da al’umma.

Sauran waɗanda aka naɗa a matsayin manyan sakatarori sun haɗa da Sulaiman Adamu Gachi daga Kankia da Muhammad Usman daga Daura.

Muƙaddashin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Katsina Malam Masa’ud Mustapha Banye yace naɗin,gwamnati ta yi imanin za suyi amfani da naɗin nasu wajen nuna ƙwarewa, jajircewa da sadaukar da kai wajan tafiyar da nauyin da aka ɗora masu domin kawo cigaba a aikin gwamnati.

Banye ya taya manyan sakatarori murna da fatan samun nasara akan nauyin da Allah ya ɗora masu.

Nan gaba ne za a sanar da ranar da za su amshi rantsuwa.

By ukarofi

Leave a Reply