Tinubu ya ƙudiri aniyar kafa cibiyar tashar jiragen ruwa a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar da busashshiyar tashar jiragen ruwa a Kebbi da yin alƙawarin ƙara bayar da wasu ayyukan titina a jihar biyo bayan buƙatar hakan da Gwamna Nasir Idris na jihar ya gabatar.

Shugaba Tinubu ya ya sanar da haka ne yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a filin wasa na Birnin Kebbi, babban birnin jihar. Taron ya samu halartar dubunnan magoya bayan APC da suka taru domin nuna goyon bayansu ga sake zaɓar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Haka kuma, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da wasu jagororin jam’iyya sun halarci taron, wanda aka gudanar da jawabai da fatan alheri daga jiga-jigan jam’iyya.

Da yake jawabi a taron, Gwamna Nasir Idris ya bayyana gamsuwa da ya yadda aka samu dandazon jama’a sun halarci taron sannan ya yi alƙawarin cewa Jihar Kebbi za ta bayar da kaso 100 na ƙuri’unta ga Tinubu a zaɓen 2027.

Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari , ya ce Tinubu ya yi aiki da dama a Arwa maso Yamma a Jihar Kebbi. A cewarsa, shugaban ya samu gagarumar tarba ne a shiyyar sakamakon muhimman ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa a yankin ciki har da babban titin Sakkwato zuwa Badagry, wanda aƙalla kilomita 200 na aiki ne zai bi ta jihar Kebbi.

A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya yi godiya ga al’ummar Kebbi bisa goyon bayansu da kuma yaba wa gwamnan jihar kan jagorancinsa, yana mai sanar da amincewarsa ga ayyukan da gwamnan ya gabatar masa, ciki har da cibiyar tashar jiragen ta Kebbi Inland Dry Port da kuma cin alwashin amince wa ƙarin wasu ayyuka titina a jiharn

By Babaji

Leave a Reply