Corticosteroids a kayan kwalliya

Spread the love

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

Wani lokaci mace kan sayi wani man shafawa ne saboda kawai an gaya mata cewa yana aiki. Ba ta san ainihin abin da ke cikinsa ba, ba ta san dalilin da ya sa canjin ya zo da sauri haka ba, kuma wataƙila ba ta ma tsaya ta tambayi kanta irin canjin da take gani a fatarta ba. Abin da ta sani kawai shi ne, tabon da take fama da shi yana raguwa, fatar ta fara yin laushi, ko kuma launin fatarta ya fara sauyawa kamar yadda take so.

Amma a wasu lokuta, abin da ya sa ake fara ganin wannan canji da sauri na iya zama wani sinadari mai ƙarfi da bai kamata a riƙa shafawa a fata ba tare da sanin abin da yake yi ba. A nan ne kalmar “yana aiki” take buƙatar a tsaya a yi mata wata tambayar ta yaya yake aiki, kuma me zai biyo bayan wannan aiki? Domin ba duka abin da ke kawo saurin canji ga fata ne yake nufin cewa fatar tana samun lafiya ba.

Idan fata ta fara rage kauri, ta fara samun tsage-tsage, kuraje ko wani canjin launi da ya fara bayyana bayan fara amfani da wani man shafawa, shin za a kau da kai daga ganin illar ne kawai saboda man ya yi abin da aka saye shi domin ya yi? Wannan ita ce tambayar da ya kamata mace ta fara yi tun kafin ta jira illar ta bayyana, domin wani lokaci abin da yake sa fata ta yi kyau a idon mai amfani a farkon lokaci, shi ne abin da zai iya jefa ta cikin wata matsala idan aka ci gaba da amfani da shi ba tare da sanin abin da yake yi ba.

Binciken da aka gudanar kan amfani da kayan sauya launin fata a Afirka ya nuna cewa hydroƙuinone, glucocorticoids da mercury na daga cikin sinadaran da aka samu da alaƙa da matsalolin da ake iya gani bayan amfani da irin waɗannan kayayyaki na dogon lokaci. Daga cikin matsalolin da aka ruwaito akwai canjin launin fata, kuraje, raguwar kaurin fata, tsagewar fata da dermatitis. A wasu yanayi, musamman idan ana amfani da sinadarai masu ƙarfi na dogon lokaci ko a manyan wuraren jiki, illar na iya wuce fata ta shafi wasu sassan jiki.

A cikin wannan jerin, corticosteroids na da wani abu na musamman da ya kamata mai amfani da kayan kwalliya ta sani. Wasu daga cikinsu na iya sa fata ta yi kama da ta samu sauƙi ko kuma ta nuna wani canji cikin sauri. Wannan saurin canjin kuwa na iya sa mai amfani ta ɗauka cewa man ya dace da ita, alhali abin da take gani ba lallai ne ya zama alamar lafiyar fata ba. A nan ne bambancin yake, fata na iya nuna canji cikin sauri, amma canjin ba shi ne lafiyar fata ba.

Saboda haka, kafin a yi farin ciki da wani mai saboda yadda ya sa fata ta sauya cikin ɗan lokaci, akwai buƙatar a san abin da yake cikin man, irin tasirin da sinadarin yake yi a fata da kuma abin da zai iya biyo baya idan aka ci gaba da amfani da shi. Domin a harkar kwalliya, ba saurin ganin sakamako ne kaɗai ya kamata ya burge mace ba; abin da ya fi muhimmanci shi ne sanin ko wannan sakamakon yana zuwa ne tare da lafiyar fatar, ko kuma wata matsala ce da ba ta fara bayyana a fili ba tukuna.

By ukarofi

Leave a Reply