Ya kulle kansa a banɗakin zamani a ranar ƙaddamarwa

Spread the love

Wani mutum ya shiga sabon banɗakin jama’a mai sarrafa kansa domin yin buƙatarsa, amma abin da bai yi tsammani ba shi ne, zai sha wahala kafin ya sake ganin hasken rana!

Mutumin bai san cewa banɗakin da ya shiga ba shi da irin ƙofofin da ake turawa ko ja da hannu ba. Bayan ya kammala buƙatarsa, sai ya kasa gano yadda zai buɗe ƙofar ya fita, lamarin da ya sa ya fara fafutukar neman mafita har ya kai ga ƙoƙarin buɗe ƙofar da ƙarfi.

Wani abin ban mamaki shi ne, banɗakin ya fi shi sanin yadda yake aiki.

Lamarin ya faru ne a birnin Chicago da ke ƙasar Amurka, inda wani mutum ya makale a cikin sabon banɗakin jama’a mai sarrafa kansa, jim kaɗan bayan ƙaddamar da shi a ranar 11 ga Nuwamba, 2026.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya shiga bandakin ne da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Laraba, domin biyan buƙatarsa. Sai dai bayan ya kammala, ya kasa fahimtar yadda zai buɗe ƙofar da kanta ke sarrafuwa.

A cewar Paul Stewart, kakakin kamfanin JCDecauɗ da ke kula da bandakin, akwai maɓallan da aka tanada domin buɗe ƙofar, tare da saƙonnin murya da ke bayyana wa masu amfani da shi yadda za su gudanar da harkokinsu.

Sai dai mutumin bai lura da maɓallin fita ba, maimakon haka sai ya fara ƙoƙarin tura ƙofar da ƙarfi, har ya kai ga harbinta da ƙafa domin ya samu damar fita.

Wannan yunƙuri nasa ya haifar da wata matsala ta fasaha, inda na’urar tsaron banɗakin ta kulle ƙofar gaba ɗaya rigif, ta yadda ba zai iya buɗe ta daga ciki ba.

Daga nan ne aka kunna tsarin neman agajin gaggawa, lamarin da ya sa jami’an tsaro da masu aikin ceto suka garzaya wurin.

Rahoton ya bayyana cewa, jami’an kashe gobara da ke kusa da wurin su ne suka fara isa, inda suka yi amfani da na’urar buɗe ƙofar daga waje, sannan aka samu nasarar fitar da mutumin.

An tabbatar da cewa mutumin bai samu rauni ba, duk da cewa ya shiga cikin tashin hankali a lokacin da yake ƙoƙarin kuɓuta daga banɗakin.

By ukarofi

Leave a Reply