INEC ta horas da ƙungiyoyi dabarun shigar masu buƙata ta musamman zaɓen 2027

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), reshen Jihar Bauchi, ta gudanar da horaswa ga masu ruwa da tsaki kan hanyoyin tabbatar da cikakken shigar masu buƙata ta musamman cikin zaɓen 2027, domin bai wa dukkan ‘yan ƙasa damar gudanar da zaɓe ba tare da fuskantar wariya ko ƙalubalen da zai hana su amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya ba.

Shirin horaswar, wanda Kwamishinan Zaɓe na REC na hukumar a jihar ya shirya, ya haɗa da wakilan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa (NOA), jami’an tsaro, ƙungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya da shugabannin addinai, wakilan jam’iyyun siyasa, ‘yan jarida da shugabannin ƙungiyoyin masu buƙata ta musamman.

An mayar da hankali a yayin taron kan dabaru, hanyoyin aiki da amfani da fasahohi da za su taimaka wajen tabbatar da cewa masu buƙata ta musamman sun samu cikakkiyar damar shiga zaɓen 2027 a matsayin masu zaɓe, ‘yan takara, jami’an gudanar da zaɓe da masu sa ido.

Hukumar ta bayyana cewa ba wai kawai ana son masu buƙata ta musamman su samu damar jefa ƙuri’a ba ne, har ma ana son a tabbatar da cewa sun shiga dukkan matakan gudanar da zaɓe, tun daga shirye-shirye har zuwa tattara sakamako da sa ido kan yadda aka gudanar da zaɓen.

Wani babban abin da ya ja hankalin mahalarta shi ne yadda ake samun matsaloli da dama da ke hana wasu masu buƙata ta musamman gudanar da zaɓe cikin sauƙi, musamman rashin hanyoyin shiga rumfunan zaɓe da kuma ƙarancin hanyoyin sadarwa da suka dace da buƙatunsu.

An bayyana misalan matsalolin da suka haɗa da masu matsalar ji waɗanda ba sa iya fahimtar umarnin jami’an zaɓe, da masu amfani da kujerun guragu waɗanda ke fuskantar wahalar shiga wasu rumfunan zaɓe saboda matakala da rashin hanyoyin hawa.

Haka kuma, masu matsalar gani na daga cikin waɗanda ke buƙatar kulawa ta musamman wajen tabbatar da cewa za su iya samun bayanan zaɓe da gudanar da ayyukan da suka shafi zaɓe ba tare da dogaro da wasu fiye da kima ba.

A yayin horaswar, muƙaddashin Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa a Jihar Bauchi, Adamu Sarkinyara, ya bayyana matakan da hukumar za ta ɗauka domin tallafa wa shirin tabbatar da zaɓe mai bai wa kowa dama.

Sarkinyara ya ce, hukumar za ta ƙara wayar da kan jama’a a matakin ƙananan hukumomi da unguwanni domin tabbatar da cewa masu buƙata ta musamman sun fahimci haƙƙoƙinsu na zaɓe da kuma muhimmancin shiga harkokin dimokuraɗiyya.

Ya bayyana cewa za a gudanar da wannan wayar da kai a dukkan ƙananan hukumomi 20 da mazabu 212 na Jihar Bauchi.

Ya kuma ce hukumar za ta shigar da saƙonnin da suka shafi haɗa kan masu buƙata ta musamman cikin shirye-shiryenta na yau da kullum, ciki har da shirin Peace Across All Eɗpectations (PAɗ), wanda manufarsa ita ce inganta zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Sarkinyara ya bayyana cewa babban saƙon da hukumar ke son isarwa shi ne cewa zaɓe na kowa ne, kuma ba ya kamata a samu wani ɗan ƙasa da za a hana amfani da haƙƙinsa na zaɓe saboda yanayin jikinsa ko wata matsala ta musamman da yake fuskanta.

Ya ce Hukumar Wayar da Kan Jama’a za ta kuma horas da jami’anta masu kula da wayar da kan al’umma domin su fahimci yadda za su taimaka wa nau’o’in masu buƙata ta musamman cikin mutunci da girmamawa.

Ya lissafa waɗanda suka haɗa da makafi, kurame, masu matsalar motsa jiki, masu matsalar fahimta, masu matsalolin lafiyar kwakwalwa da kuma masu matsalar launin fata ta musamman (zabiya).

Ya ƙara da cewa hukumar za ta yi aiki tare da ƙungiyar Disability Connection and Community Development Foundation (DCCDF), Hukumar INEC, ƙungiyar Haɗin Kan Masu Buƙata ta Musamman ta ƙasa (JONAPWD), sarakunan gargajiya da shugabannin addinai domin tabbatar da cewa rumfunan zaɓe sun dace da buƙatun kowa.

Haka kuma, hukumar za ta riƙa sa ido kan yadda masu buƙata ta musamman suka shiga zaɓe a ranar gudanar da shi, tare da tattara bayanai kan adadinsu, matsalolin da suka fuskanta da kuma wuraren da ake buƙatar ingantawa.

Sarkinyara ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da kare lafiyar masu buƙata ta musamman a ranar zaɓe, tare da buƙatar jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su shigar da muradunsu cikin manufofi da shirye-shiryen kamfen ɗinsu.

Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su ƙara wayar da kan jama’a kan muhimmancin bai wa masu buƙata ta musamman damar shiga harkokin zaɓe, domin tabbatar da cewa ba a ware su daga tsarin dimokuraɗiyya ba.

By ukarofi

Leave a Reply