Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, ya danganta yawan magoya baya da mambobin jam’iyyar APC da suka halarci taron yaƙin neman zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya a Jos, Jihar Filato, da abin da ya kira ƙaruwar godiyar jama’a ga nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin shekaru ukun da suka gabata.
Da yake jawabi a wajen taron a ranar Asabar, Ministan ya ce yadda magoya baya da mambobin jam’iyyar suka halarta cikin murna yana nuna amincewa da shirin gyare-gyaren gwamnatin da ƙoƙarin ta na sake daidaita ƙasar nan domin samun cigaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya ce: “Dafifin jama’ar da muke gani a nan yau shaida ce ƙarara ta amincewar da ‘yan Nijeriya ke da ita ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma alƙiblar da gwamnatin sa ta dosa da ƙasar nan. Jama’a suna ganin ƙoƙarin da ake yi na magance matsalolin da suka daɗe, ƙarfafa tattalin arziki da samar da makoma mafi kyau ga ƙasar mu.
Idris ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da suka haɗa da ƙarfafa tattalin arziki, faɗaɗa ababen more rayuwa, samar da damarmaki da inganta yanayin rayuwar ‘yan Nijeriya.
Ya ce gwamnatin ta mayar da hankali kan tabbatar da nasarorin gyare-gyaren ta da tabbatar da cewa amfanin su ya zama ingantattun sauye-sauye a rayuwar jama’a a faɗin ƙasar nan.
“Shugaba Tinubu yana nan daram kan manufar sa, kuma yana tabbatar da cewa shawarwarin da ake yankewa a yau za su kawo alheri mai ɗorewa ga ‘yan Nijeriya. Abin da ke da muhimmanci shi ne mu ci gaba da ɗorawa kan cigaban da aka samu, mu yi aiki zuwa ga gina ƙasa mai ƙarfi da wadata,” inji shi.
Ministan ya buƙaci jam’iyyun adawa da su rungumi yaƙin neman zaɓe bisa batutuwa da kuma nuna cikakken shiri na tsari, maimakon dogaro da maganganun siyasa da sukar gwamnati.
Ya jaddada cewa tsarin dimokiraɗiyyar Nijeriya zai fi amfana da haɗin kai na siyasa mai ma’ana, amintattun madadin shugabanci da muhawara mai zurfi kan manufofi da shirye-shiryen da ke shafar walwalar ‘yan Nijeriya kai-tsaye.
Idris ya ƙara jaddada muhimmancin gudanar da siyasa cikin nauyi yayin da ƙasar nan take dosar babban zaɓen 2027, yana mai cewa jam’iyyun siyasa suna da haƙƙin haɗin gwiwa na tallata shiga cikin lumana da ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin dimokiraɗiyya.
Haka kuma, a wajen taron, Ministan Raya Ma’adanai, Dakta Dele Alake, ya nanata muhimmancin dabarun yankin Arewa ta Tsakiya ga zaman lafiyar siyasar Nijeriya, cigaban tattalin arziki da cigaban ƙasa.
Ya bayyana irin gagarumar damar da yankin yake da ita, musamman a fannin ma’adanai masu ƙarfi da sauran ɓangarorin samar da arziki, tare da jaddada muhimmancin sa ga sauyin tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.
Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Kafafen Yaɗa Labarai da Sadarwar Jama’a, Mista Sunday Dare, ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin ɗan dimokiraɗiyya mai jajircewa wanda aikin sa na siyasa yana nuna dogon lokaci na shiga cikin cigaban dimokiraɗiyyar Nijeriya.
Ya sake jaddada jajircewar APC ga shiga siyasa cikin lumana, yana mai cewa jam’iyyar ba ta goyon bayan tashin hankali kuma tana nan daram kan ƙa’idojin dimokiraɗiyya.
Taron na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Arewa ta Tsakiya ya haɗa shugabannin jam’iyya, jami’an gwamnati, masu ruwa da tsaki da magoya baya daga faɗin yankin, a matsayin wani ɓangare na ayyukan yaƙin neman zaɓe na APC a faɗin ƙasar nan gabanin babban zaɓen 2027.
