Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya aza harsashin gyara da ɗaukaka darajar Asibitin garin Ingawa da zai ci kuɗi Naira biliyan 1.4b.
Kwangilar da aka bai wa kamfanin Global Fama zai samar da ƙarin gine gine da na’urorin kiwon lafiya wanda bayan kammala aikin, Asibitin zai daidaita da sauran manyan asibitoci da ke jihar.
Gwamna Raɗɗa ya kuma ƙaddamar da aikin hanya mai tsawon kilomita 1.65km a cikin garin Ingawa wanda ƙaramar hukumar Ingawa ke ginawa.
A jawabinsa Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana aikin hanyar a matsayin ɗaya daga cikin romon dimokraɗiyya da Gwamnan ya ce ya nuna nasarar tsare tsare da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙira.
“Ba ƙananan hukumomi yanci ƙarƙashin Bola Tinubu ya ƙarfafa masu aiwatar da ayyuka na raya ƙasa da al’ummar su ke buƙata,” yace.
Ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar da masu ruwa na yankin basa nasarar kammala aikin hanyar da ya bayyana cewa zai bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin yankin.
