
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Alhaji Ɗahiru Ahmed Malabu, wanda shi ne mahaifin Sanata Aishatu Ɗahiru Ahmed Binani, ya rasu a Abuja bayan shafe shekaru 81 a duniya. Malabu, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne kuma mahaifin ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa, ya rasu ne a ranar Juma’a, bayan wani gajeren rashin lafiya.
Adamu Ibraheem Jimeta, wanda mataimaki ne ga Sanata Binani, ne ya tabbatar da labarin ga ‘yan jarida, inda ya ce marigayin ya rayu da ‘ya’ya tara. Daga cikin ‘ya’yan nasa akwai Sanata Aishatu Binani da Aminatu Ɗanjuma Goje, wato matar Sanata Ɗanjuma Goje.
Ibraheem Jimeta ya ce za a gudanar da jana’izarsa ne a yau Asabar da misalin ƙarfe 1:30 na rana a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja. Tsohuwar Sanatar ta sanar da rashin mahaifin nata ne cikin alhini a wani saƙon Facebook, inda ta bayyana jimamin al’amarin.
