Yadda ƙofar jirgin Triton Aviation ta ɓalle a sararin samaniya a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Binciken Haɗurran Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NSIB) ta bayyana cewa ƙofar shiga wani jirgin sama mai zaman kansa mallakin kamfanin Triton Aviation ta ɓalle ne a lokacin da jirgin ke tashi sama daga Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Binciken farko ya kuma nuna cewa dukkan na’urorin kulle ƙofar suna a buɗe a lokacin da lamarin ya faru. An ruwaito cewa wannan bayani na ƙunshe ne cikin rahoton farko da hukumar ta fitar kan haɗarin da ya shafi jirgin samfurin Bombardier Challenger 604, kamar yadda Babban Daraktan Hukumar, Aleɗ Badeh, ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Jirgin ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Abuja jim kaɗan bayan ƙofarsa ta ɓalle a sararin samaniya a ranar 15 ga Oktoba. A cewar rahoton farko, jirgin mai lambar aiki DWC052 yana gudanar da zirga-zirgar jirgi ta musamman ba tare da tsayayyen jadawali ba daga Abuja zuwa Filin Jirgin Sama na ƙasa da ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas. Mutane tara ne ke cikinsa, waɗanda suka haɗa da ma’aikatan tuƙin jirgi biyu, ma’aikacin kula da fasinjoji guda ɗaya da fasinjoji shida.

Rahoton ya ce, “Da misalin ƙarfe 5:19 na yamma agogon gida, a lokacin da jirgin ke fara hawa sama, ma’aikatan tuƙinsa sun lura cewa tsayin da ake auna shi a cikin ɗakin fasinjoji ya ƙaru ba bisa ƙa’ida ba. Hakan ya sa suka yi zargin cewa akwai matsala a tsarin daidaita matsin iska a cikin jirgin.”

Rahoton ya ci gaba da cewa, “Daga bisani, kyaftin ɗin jirgin ya umarci ma’aikacin kula da fasinjoji da ya sake duba babbar ƙofar ɗakin fasinjoji domin tabbatar da cewa tana kulle yadda ya kamata. Amma yayin da ma’aikacin ke tunkarar ƙofar da ke tsakanin ɗakin fasinjoji da ma’aikatan jirgi domin gudanar da binciken, sai ƙofar ta buɗe, daga bisani kuma ta ɓalle daga jikin jirgin. “Ma’aikatan tuƙin jirgin sun ayyana yanayin gaggawa, sannan suka tuntuɓi masu kula da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin Abuja (ATC), domin samun izinin komawa filin jirgin nan take. Jirgin ya sauka lafiya a titin saukar jiragen sama mai lamba 22 da misalin ƙarfe 5:34 na yamma agogon gida. Dukkan mutane tara da ke cikin jirgin sun fita ba tare da wani rauni ba. Sai dai jirgin ya samu babbar illa.”

NSIB ta ce, nan take ta tura masu bincike zuwa wurin da lamarin ya faru bayan samun rahoton aukuwar haɗarin a ranar. An ɗora wa tawagar alhakin bincike da gano ƙofar da ta ɓalle, dawo da ita, tare da fara tantance abubuwan da suka faru bayan haɗarin.

Hukumar ta bayyana cewa binciken ƙofar da aka yi ya nuna cewa alamar da ke nuna matsayin makullinta tana kan jan launi mai ɗauke da rubutun “UNLOCKED”, wanda ke nufin ba a kulle ƙofar ba. Haka kuma, an gano cewa hannayen buɗe ƙofar na ciki da na waje, da kuma dukkan na’urorin makullinta, suna a buɗe.

Binciken ya kuma gano cewa ɓangaren ƙasan jikin jirgin ya samu lahani, ciki har da na’urar sadarwar rediyo mai matuƙar muhimmanci (VHF) da kuma sashen da ake ajiye mai.

Hukumar ta ƙara da cewa wasu sassan gonar masara sun lalace sakamakon lamarin. Haka kuma, NSIB ta bayyana cewa ma’aikatan tuƙin jirgin ba su ji wata ƙarar gargaɗi ko ganin wata alamar gargaɗi da ke nuna matsalar ƙofar ba kafin aukuwar lamarin. Bugu da ƙari, bayanan kwamfutar da ke tantance matsalolin fasaha na jirgin ba su nuna cewa an samu wata matsala ko gargaɗi da ya shafi ƙofar ba.

Hukumar ta ce, bincike na gaba zai haɗa da gwaje-gwajen ƙarafa da kuma zurfafa bincike kan ƙofar da ta ɓalle, na’urorin kulle ta da sauran tsarin lantarki da ke da alaƙa da ita. Ta ce manufar waɗannan ƙarin bincike ita ce gano ko wata matsala ta na’ura ko ta tsarin ginin ƙofar da jirgin ce ta taimaka wajen haddasa aukuwar lamarin.

By ukarofi

Leave a Reply