UNICEF ta gano yara marasa zuwa makaranta 624,000 a Sakkwato, Kebbi da Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ta koka akan yadda ake cigaba da fuskantar koma-baya a fannin ilimi a Jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, inda ta ce aƙalla yara 624,000 ne ba sa zuwa makaranta a sassan jihohin.

UNICEF ta ce guda 68,000 ne zuwa yanzu ta samu damar tallafa wa wajen sanya su a makaranta. Shugaban hukumar na ofishinta a jihar Sakkwato, Dakta Michael Juma ne ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin bayar da ba’asi ga ‘yan jarida a Sakkwato domin karrama Ranar Yara ta Duniya ta 2026.

Ya ce, ratar da ke tsakanin yaran da aka gano da waɗanda suka samu shiga cikin tallafin ta nuna cewa akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙaimi, zuba jari da damawa da al’umma wajen magance matsalolin rashin zuwa makaranta acikin yara ƙanana.

Akan haka ne ya kuma buƙaci ‘yan jarida da su ƙarfafa wa ayyukan ruwaito rahotanni akan ‘yancin yara, haska lamuran tsayar da gaskiya da adalci da tabbatar da cewa matsalolin da yara suke fuskanta ya samu kulawar da ta dace.

Musamman UNICEF ta sanar da cewa jimillar yara 98,000 ne a sassan jihohin suka amfana daga shirin Teaching at the Right Level (TaRL), wato koyarwa a matakin da ya dace, wanda ya mayar da hankali akan inganta karatu a matakin tushe da ilimin lissafi.

A cewarsa, UNICEF tana kuma tallafa wa ci-gaban malamai, samar da kayan koyon karatu, bunƙasa ilimin matakin farko, tsara ilimin Al-Ƙur’ani da samar da wasu fagagen karatu, ciki har da samun ilimi ta rediyo da kuma fasfo ɗin koyon karatu.

A game da lafiya, Dakta Juma ya bayyana cewa, kusan yara ƙanana miliyan 7.8 aka yi wa allurar rigakafin ƙyanda a Sakkwato, Kebbi da Zamfara, yana mai cewa yara 624,000 ne aka gano ba sa zuwa makaranta a jihar.

By Babaji

Leave a Reply