Yadda masu Adaidaita ke jefa rayukan jama’a cikin haɗari a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A Nijeriya, adaidaita sahu, wanda akan kira da Napep, ya zama ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri, musamman a birane kamar Abuja, inda dubban mutane ke amfani da shi wajen zirga-zirgar yau da kullum. Sai dai, duk da muhimmancin wannan hanya ta sufuri, ana ƙara nuna damuwa kan yadda wasu masu tuƙin sa ke gudanar da sana’ar ba tare da ingantaccen horon tuƙi ko lasisin da doka ta tanada masa ba.

Wani mummunan haɗari da ya rutsa da matashi ɗan shekara 18, Efe Solomon, a Abuja, ya sake fito da wannan matsala fili. Solomon ya samu munanan raunuka sakamakon karo da adaidaita sahu, har ta kai ga likitoci sun buƙaci a yi masa tiyata cikin gaggawa domin ceton ƙafarsa.

Wannan lamari ya haifar da tambayoyi masu muhimmanci game da yadda ake ba da izinin gudanar da wannan sana’a, irin horon da masu tukin ke samu, da kuma matakan da hukumomin da abin ya shafa ke ɗauka domin kare rayukan fasinjoji da sauran masu amfani da tituna.

Efe Solomon ya gama shan rawa sosai a wani bikin ƙungiyar ɗalibai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Yana cikin farin cikin shagalin bikin ne lokacin da ya zauna a bayan abokin karatunsa wanda ke tuƙin babur. Da misalin ƙarfe 5:00 na asuba, suka kama hanyar komawa ƙofar makarantar. Lokacin saura ‘yan kwanaki kaɗan Kirsimeti a shekarar 2025, kuma titin babu cunkoson ababen hawa.

Kwatsam sai aka ji wani mummunan ƙara sakamakon taho-mu-gama. Wata babbar adaidaita sahu, wadda aka fi sani da Keke NAPEP, ta yi karo da su. Direban adaidaita sahun yana tafiya ne a kan titin da ya saɓa wa alƙiblar zirga-zirga, ba tare da kunna fitilun babur ɗin ba. Kafin Solomon da abokinsa su samu damar kaucewa, tuni haɗarin ya auku.

Cikin ƙanƙanin lokaci, farin cikin Solomon ya rikiɗe zuwa mummunan rauni. ƙashinsa ya karye, yayin da naman jikinsa da ke saman gwiwar ƙafarsa ta hagu ya tsage, har aka samu babban rauni da ya bayyana a fili.

Wasu mutanen da suka halarci bikin kuma suke kusa da wurin haɗarin sun garzaya da shi zuwa Asibitin ƙwararru na Allied Specialist da ke Gwagwalada. “Da na isa asibitin, sai na ga jini ko’ina,” inji Fatima Efe, ƙanwar Solomon, wadda ta kasa riƙe hawayenta yayin da take tuna abin da ya faru a wannan safiyar. Solomon ya tuna yadda ya riƙe hannun ƙanwarsa yana cewa: “ƙanwata, ƙanwata, kada ki damu, ba zan mutu ba. A wannan lokacin na shiga ruɗani. Ban san abin da zan ce ba. Sai kawai na fashe da kuka,” inji Fatima.

Iyalin Solomon sun sake fuskantar wata babbar matsala a asibitin. Fatima ta ce likitan da ke bakin aiki ya sanar da ita cewa dole ne su tara kuɗin da ya kai naira miliyan 1.5 domin yi wa Solomon tiyata cikin gaggawa, in ba haka ba za a yanke masa ƙafa. “Solomon yaro ne ƙarami. Shekarunsa 18 kacal. Ka yi tunanin matashi mai shekara 18 da ƙafa guda ɗaya kawai,” inji Fatima, tana share hawayen da suka cika idanunta.

Zargin da ake yi wa masu tuƙin adaidaita sahu da abin da doka ta tanada:

Yayin da iyalan Solomon ke fafutukar ganin an ceci ƙafarsa, ana ci gaba da yaɗa iƙirarin cewa masu tuƙin adaidaita sahu a Nijeriya suna gudanar da sana’arsu ne ba tare da horo ko lasisin tuƙi ba.

A ranar 10 ga Maris, 2023, wani mai amfani da dandalin sada zumunta na ɗ mai suna Odu Obodumu ya wallafa wani saƙo a shafinsa, inda ya yi zargin cewa masu tuƙin adaidaita sahu na kasuwanci a Nijeriya ba su da lasisin tuƙi. Ya rubuta cewa, “Har yanzu ba mu fara ba. Masu tuƙin Keke NAPEP ba su da lasisin tuƙi, kuma babu wanda ya damu da hakan. Barazana ce a kan tituna. Ba su san komai game da dokokin zirga-zirga ba. Wane rukuni ne na lasisi ya kamata su mallaka? Na taɓa tambayar wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa (VIO) da ya tsayar da ni wata rana, amma shi ma bai sani ba. Sai ya ce an yi musu rajista. Shin rajista ita ce lasisi?”

A watan Maris na 2024, Obodumu ya sake wallafa wani saƙo, a matsayin martani ga wani mai amfani da dandalin wanda ya koka kan yadda masu tukin adaidaita sahu ke tuƙi cikin ganganci a Abuja. A wannan karon ma, ya sake jaddada zargin da ya yi a shekarar 2023. “Masu tuƙin adaidaita sahu ba su da lasisi. Wane rukuni ne na lasisi suke da shi? Ba rukuni na A na masu babura ba, ba na masu tuƙin kowace irin mota ba, kuma ba na manyan motocin dakon kaya masu tirela ba. Don haka, suna tuƙi ne ba tare da lasisi ba,” inji shi.

Baya ga Obodumu, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta da dama sun wallafa saƙonni daban-daban suna tambayar ko ana horar da masu tukin adaidaita sahu a Nijeriya, ko kuma suna samun lasisin tuƙi kafin fara aiki.

Sai dai, abin da dokokin Nijeriya suka tanada a rubuce ya nuna cewa duk wanda zai tuka kowace irin mota a kan titunan jama’a dole ne ya samu horon da ya dace tare da lasisin tuƙi. Misali, sashe na 23(1)(9) na Dokar Kafa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta shekarar 2007 ya tanadi cewa ba wanda aka yarda ya tuka kowace irin mota a kan titunan Nijeriya ba tare da lasisin tuƙi ba.

ƙaramin sashe na biyu na dokar ya kuma bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin karya wannan doka, bayan tabbatar da laifinsa a kotu, zai biya tarar naira 10,000. Haka kuma, wa’ida ta 46(5) ta Dokokin Zirga-zirgar Ababen Hawa na ƙasa (NRTR) ta shekarar 2012 ta ce: “Duk mutumin da ba shi da lasisin tuƙi, ko kuma wanda bai kai shekara 18 ba, ya tuka mota ko babur a kan titin jama’a, ya aikata laifi. Idan aka same shi da laifi a kotu, zai biya tarar naira 5,000.”

Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) tana bayar da lasisin tuƙi iri-iri bisa nau’in ababen hawa da kuma rukunin masu amfani da tituna. Ana saka masu tuƙin babura da masu tuƙin adaidaita sahu a rukuni na A.

A farkon shekarar 2026, Mataimakin Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa, Olusegun Ogungbemide, wanda a lokacin yake riƙe da muƙamin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, kafin daga bisani ya yi ritaya, ya tabbatar wa DUBAWA cewa doka ba ta amince da duk wani mai tukin adaidaita sahu na kasuwanci ya yi aiki a titunan Nijeriya ba tare da lasisi ba. Sai dai, domin samun lasisin tuƙi, ƙa’idoji na 45(1), 57(1) da 45(3)(a) na Dokokin Zirga-zirgar Ababen Hawa na Ƙasa na shekarar 2012 sun wajabta wa masu neman lasisi su samu horo a makarantar koyon tuƙi da gwamnati ta amince da ita, sannan Hukumar Binciken Ingancin Ababen Hawa (VIS) ta yi musu gwaji.

Ganin yadda iƙirarin da ake yaɗawa a bainar jama’a ya saɓa wa abin da dokoki da hukumomin da ke tabbatar da bin doka suka tanada, sai aka yi tambaya: Shin zai yiwu ɗaruruwan masu tuƙin adaidaita sahu da ke jigilar dubban fasinjoji a Babban Birnin Tarayya ba su da horon tuƙi, kuma Hukumar Kiyaye Haɗurra ba ta ba su lasisi ba?

Masu tuƙin adaidaita sahu a Abuja ba su da lasisi ko ingantaccen horon tuƙi:

Domin tantance sahihancin wacannan zarge-zarge, DUBAWA ta kai ziyara unguwannin Kubwa, Gwarinpa, Apo Gudu da Nyanya da ke Babban Birnin Tarayya, inda ta yi hira da masu tukin adaidaita sahu guda 20 da aka zaɓa ba tare da wani tsari na musamman ba. Dukkaninsu sun ba da amsa iri ɗaya: Babu wanda ke da lasisin tuƙi na Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa. Maimakon haka, suna gudanar da sana’arsu ne da katin shaidar zama mambobin ƙungiyar masu tukin adaidaita sahu.

Lokacin da DUBAWA ta tambayi wani mai tuƙin adaidaita sahu a Nyanya mai suna Aminu Rabiu ko jami’an hukumar kiyaye haɗurra suna tsayar da shi domin neman lasisin tuƙi, sai ya amsa a sauƙaƙe da cewa:  “A’a, hukumar kiyaye haɗurra ba ta tsayar da ni. Ba ni da lasisi, katin shaida kawai nake da shi.”

Aminu Rabiu, mai tukin adaidaita sahu a Nyanya, yana nuna katunan shaidar ƙungiyarsa (Hoto: Sunday Awosoro). Daga nan sai aka tambaye su yadda suka koyi tukin adaidaita sahu. Dukkan masu tukin 20 sun ce sun koyi sana’ar ne ta hanyar rakiyar yayyensu ko abokansu na ’yan sa’o’i kaɗan, kafin su fara ɗaukar fasinjoji domin su ci gaba da koyon tuƙin a aikace.

Musa Bello, wani mai tuƙin adaidaita sahu a Kubwa, ya ce, “Na gama makaranta, amma ban samu aikin yi ba. Sai ɗan uwana ya kira ni ya ce, idan ba ni da wani abin yi a gida, na zo na fara wannan sana’a domin in riƙa gudanar da rayuwata har sai na samu aikin gwamnati. Wata rana ya hau da ni cikin hanya, ya koya min yadda ake tuƙi.”

Shi ma Muhammed Bello, wani mai tuƙin adaidaita sahu a Apo Gudu, ya ce, “Ina da wani ɗan uwa a lokacin da na zo Abuja. Sai ya ce in zo in tuƙa adaidaita sahun, kuma shi ne ya koya min.”

An buga hotunan alamomin zirga-zirgar ababen hawa guda 10 a takarda, sannan aka bai wa masu tuƙin adaidaita sahun domin su bayyana ma’anar kowace alama. Alamomin sun haɗa da ta dakata, fitilun kula da zirga-zirga, gargadin tudu a hanya, hana wucewa, iyakar gudun mota, hana yin fakin, hana juya hagu, hana juya dama, gargaɗin mahaɗar hanyoyi a gaba da kuma gargaɗin zamewar hanya.

Daga cikin masu tuƙin adaidaita sahu 20 da aka gwada, babu wanda ya iya gane ma’anar alamomin iyakar gudun mota da kuma zamewar hanya. Mutane biyu kacal suka iya fassara ma’anar launuka uku na fitilun kula da zirga-zirga yadda ya kamata. Biyar daga cikinsu ne suka gane alamar gargaɗin tudu a hanya, yayin da 16 ba su san ma’anar alamar hana wucewa ba.

A jimlace, kashi 90 cikin 100 na masu tukin da aka gwada sun kasa gane fiye da biyu daga cikin alamomin hanya guda 10 da aka nuna musu. Da aka tambaye su dalilin rashin sanin waɗannan alamomi, sai suka ce ba wanda ya taɓa koya musu su.

‘Ba zai yiwu a horar da duk masu tuƙin adaidaita sahu tare da ba su lasisi lokaci guda ba’ – FRSC:

Mataimakin Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa, Ogungbemide, ya ce ba zai yiwu a tilasta wa dukkan masu tukin adaidaita sahu su samu horo ko lasisi a lokaci guda ba.

Ya bayyana cewa an samar da adaidaita sahu ne domin cire babura daga kan tituna, saboda haɗarin da suke haifarwa ga sauran masu amfani da hanya.

A cewarsa, bayan an hana wasu masu tuƙin babura ci gaba da sana’arsu, sun koma tuƙin adaidaita sahu. Amma sai suka ci gaba da amfani da irin salon tuƙin ganganci da suka saba da shi a lokacin da suke tuƙin babura.

Ya ce, “Idan aka yi la’akari da yawan Keke NAPEP da muke da su a ƙasar nan a yau, zai zama kamar rashin ɗa’a ne in zauna a nan ina yaudarar ku da cewa za a iya sa dukkaninsu su samu lasisi a rana guda. Babu shakka, kun san cewa hakan zai ɗauki lokaci.”

By ukarofi

Leave a Reply