Wike ya buƙaci a hana ADC da NDC samun kashi 25 na ƙuri’u a Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bukaci mambobin gamayyar Rainbow Coalition su tabbatar da cewa jam’iyyun ADC da NDC ba su samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a Abuja ba a zaɓen 16 ga Janairun 2027.

Wike ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC da Rainbow Coalition a babban birnin tarayya.

Ministan, wanda shi ne kodinetan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Abuja, ya gargaɗi mambobin kwamitin da kada su ɗauka cewa tuni sun yi nasara, yana mai cewa zaɓen dama ce ta nuna ƙarfin siyasar APC a yankin.

Ya bukaci mambobin kwamitin su mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a kan ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar a Abuja.

Wike ya ce gwamnatocin da suka shugabanci ƙasar tsakanin 1999 da 2023 sun bayar da takardun mallakar filaye (C of O) kimanin 7,000 zuwa 8,000, yayin da gwamnatin Tinubu ta bayar da sama da 20,000 cikin shekaru uku.

Ya kuma lissafa kafa Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Abuja, naɗa Shugaban Ma’aikata, ɗaukaka wasu ma’aikata zuwa matsayin manyan sakatarori da kuma samar da sakatariyoyin kula da harkokin mata da matasa cikin nasarorin gwamnatin Tinubu.

Haka kuma, ya ce Tinubu ne shugaban ƙasa na farko da ya bai wa Abuja wakilci a Majalisar Zartarwa ta Tarayya, shekaru 50 bayan kafa birnin a 1976.

A nasa jawabin, shugaban APC na Abuja, Ishaku Tanko Yamawo, ya ce ayyukan da Wike ya gudanar sun zama muhimmin saƙon da jam’iyyar ke amfani da shi wajen yaƙin neman zaɓe.

Shi ma shugaban PDP na Abuja, Ismaila Mohammed Dogara, ya ce tsarin haɗin gwiwar da aka samar zai ci gaba da aikin wayar da kan masu zaɓe ko da Wike ba ya yankin a ranar zaɓe.

By ukarofi

Leave a Reply