Fashin Offa: Za a gurfanar da Saraki da Ahmed a 3 ga Disamba yayin da cece-kuce ya zurfafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Osulale Ajayi na Babbar Kotun Jihar Kwara da ke ilorin, ya yanke hukuncin cewa, waɗanda ake ƙara na ɗaya da na biyu a shari’ar fashin Offa da ke gudana, wato tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Dakta Abubakar Bukola Saraki da tsohon Gwamnan Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed, ba za gurfanar da su ba har sai an gabatar musu da tuhume-tuhumen da ake da su akan shari’ar yadda ya dace.

Alƙalin ya yi wannan hukunci ne kan ababen da ake tataɓurza akansu a shari’ar bayan an gine hukunci a zaman da aka yi a baya sakamakon muhawara da aka gabatar d a ga masu ƙara da ɓangare masu kare waɗanda ake ƙara.

A zaman da aka sake yi kan al’amarin, Mai Shari’a Ajayi ya karanto hukunce-hukuncen kotun kuma ya umarci a gabatar wa mutane biyu rahoton ababen da ake tuhumarsu a kai a ranar 20 ga Nuwamba ko kafin haka, yayin da kuma ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 3 ga Disamba, 2026 da kuma aikin gurfanarwa.

Masu gabatar da ƙara sun buƙaci kotu ta bari a fara shari’ar ta hanyar gurfanar da mutane huɗun da ake ƙara, buƙatar da ba ta samu amincewar kotun ba ganin cewa ba a gabatar wa jagororin siyasa biyun ba tuhume-tuhume a hukumance.

Wannan na da alaƙa da fashin da aka yi a garin Offan Jihar Kwara na ranar 5 ga Agustan 2018, a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hare-hare a bankunan ‘yan kasuwa da hedikwatar ‘yan sanda, inda suka halaka sama da mutane 30, ciki har da ‘yan sanda da fararen hula.

By Babaji

Leave a Reply