Rikicin siyasa da ke tsakanin Gwamna Raɗɗa da Ibrahim Masari ya ɗauki sabon salo

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rikicin siyasa tsakanin Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, da mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya sake ɗaukar sabon salo bayan ’yan sanda sun sake gayyatar jami’an tsaron gwamnan, ciki har da jami’in tsaronsa (CSO), SP Abdulganiyu, da mai taimaka masa (ADC), DSP Hassan Bello, domin yi musu tambayoyi.

Akwai kuma rahotannin cewa an gayyaci shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Abdulkadir Mamman Nasir, amma mai magana da yawun gwamnan ya musanta kama shi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an tsaron biyu ba a gan su a Katsina ba tun ranar Litinin, bayan da aka ce hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Abuja ta sake gayyatar su.

Wannan na zuwa ne watanni bayan da aka yi musu tambayoyi kan zargin lalata allunan tallan siyasa da ke ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu da wasu manyan ’yan siyasar jihar.

By ukarofi

Leave a Reply