Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB) ta ƙaddamar da wani sabon tsarin da zai bai wa ɗalibai damar sauya jami’o’i ko kwasa-kwasan da suka zaɓa ba tare da zuwa ofisoshinta ko cibiyoyin da ta amince da su ba.
A cewar hukumar, wannan mataki na cikin ƙoƙarin sauƙaƙa samun damar amfani da ayyukanta, tare da samar da sauƙi ga ɗalibai ta hanyar amfani da fasahar zamani.
JAMB ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yarjejeniya na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ya fitar a safiyar Laraba, inda ya ce sabon tsarin zai ba ɗalibai damar fara da kammala sauya jami’a ko kwas ta yanar gizo daga gidajensu.
Hukumar ta ce wannan sabon tsari ya yi daidai da manufar Gwamnatin Tarayya ta sauƙaƙa harkokin kasuwanci da gudanar da ayyuka (Ease of Doing Business), da kuma burin magatakardar hukumar, Farfesa Segun Aina, na mayar da ita hukuma mai mayar da hankali kan inganta ayyuka ga al’umma.
Ta bayyana cewa sabon tsarin zai kawar da zirga-zirgar da ba ta zama dole ba zuwa ofisoshinta, rage cunkoso, tare da rage kuɗin sufuri, ɓata lokaci da wahalhalun da ɗalibai ke fuskanta wajen jiran samun hidima.
A ƙarƙashin sabon tsarin, ana buƙatar ɗalibai su shiga shafin JAMB e-Facility ta adireshin https://efacility.jamb.gov.ng, sannan su shiga asusunsu ta amfani da adireshin imel da kalmar sirrin da suka yi rajista da su.
Daga nan za su zaɓi sashen ‘Corrections and Uploads’ da ke gefen shafin, sannan su danna ‘Change of Programme/Institution’, su zaɓi UTME da shekarar jarabawar da ta dace.
Bayan fara biyan kuɗi, za a tura su zuwa shafin biyan kuɗi na CREDO domin kammala ciniki ta amfani da katin ATM ko tura kuɗi daga banki.
Hukumar ta shawarci ɗalibai da su koma cikin asusunsu na JAMB bayan biyan kuɗin, domin tabbatar da cewa matsayin cinikin ya koma ‘PAID (Not Used)’ kafin su ci gaba.
Bayan haka, za su shigar da bayanan sabuwar jami’a ko kwas ɗin da suke so, sannan su tabbatar da cinikin ta hanyar amfani da lambar sirri ta lokaci guda (OTP) da za a aika zuwa adireshin imel ɗinsu na rajista.
Bayan kammala tabbatarwar cikin nasara, za su danna maɓallin ‘SAVE’ domin aika buƙatar sauyin, sannan su karɓi saƙon tabbatar da cewa an yi nasarar sauya jami’a ko kwas ɗin.
Hukumar ta kuma umarci ɗalibai su buga takardar shaidar sauya jami’a ko kwas (Change of Programme/Institution Slip), sannan su shiga tsarin tantance shiga jami’o’i na tsakiya (CAPS) domin tabbatar da cewa sauyin ya bayyana a cikin bayanansu.
JAMB ta buƙaci ɗalibai su bincika zaɓin sabuwar jami’a da kwas ɗin da suka yi a hankali kafin adana bayanan, domin guje wa kuskure.
Haka kuma, ta shawarce su da su tabbatar matsayin biyan kuɗinsu ya koma ‘PAID (Not Used)’, tare da tabbatar da cewa suna iya shiga adireshin imel ɗin da suka yi rajista da shi domin karɓar lambar OTP da ake buƙata wajen tabbatar da aikin.
Hukumar ta jaddada cewa ɗalibai su gudanar da aikin da kansu ta cikin asusunsu na JAMB, tare da kiyaye bayanan shiga asusunsu da lambobin OTP daga shiga hannun wasu.
Ta kuma gargaɗi ɗalibai da su guji amfani da ’yan tsaka-tsaki ko biyan wasu mutane kuɗi domin yi musu aikin, tana mai cewa kowa zai iya kammala aikin cikin sauƙi da kansa.
Magatakardar hukumar, Farfesa Aina, ya sake jaddada aniyar JAMB na amfani da fasahar zamani wajen sauƙaƙa ayyukanta da inganta hidimomin da take bayarwa, ba tare da la’akari da inda ɗalibai suke ba.
Ya ce babban burin hukumar shi ne gina tsari mai saurin amsawa da amfani da fasahar zamani, inda ɗalibai za su rage lokacin neman hidima, su fi mayar da hankali kan cimma burinsu na ilimi.
Hukumar ta bayyana sabon tsarin a matsayin wani muhimmin ci gaba a shirinta na sauya ayyukanta zuwa tsarin dijital, inda ta ce ɗalibai za su iya sauya jami’o’i ko kwasa-kwasansu daga kusan ko’ina, muddin suna da damar amfani da intanet da kuma asusunsu na JAMB.
