Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Cibiyar Koyar da Aikin Hajji ta Nijeriya (HIN) ta ɗauki wani muhimmin mataki na ƙarfafa hulɗar ƙasa da ƙasa, biyo bayan wata ganawa mai muhimmanci da Bankin Raya Musulunci (IsDBI) da ke Jeddah, Saudiyya.
Rector na HIN, Farfesa Nasiru Maiturare, tare da Mataimakinsa, Farfesa Wasiu Gabadeen, sun kai ziyarar ban-girma ga Darakta-Janar na IsDBI, Dakta Sami Al-Suwailem, domin tattauna hanyoyin samar da haɗin gwiwa a fannonin gudanar da bincike tare, horarwa ta musamman ga ƙwararru, bunƙasa ƙwarewar hukumomi da samar da sabbin dabarun inganta gudanar da ayyukan Hajji da Umara.
A yayin ganawar, IsDBI ta bayyana aniyarta ta tallafa wa HIN ta hanyar haɗin gwiwar bincike da kuma yiwuwar bayar da tallafin kuɗi, musamman kan binciken da ya shafi tattalin arzikin aikin Hajji.
Haka kuma, cibiyar ta yi alƙawarin bayar da tallafin fasaha wajen samar da tsarin koyarwa ta yanar gizo (e-learning), domin sauƙaƙa gudanar da shirye-shiryen horar da masu ruwa da tsaki a harkokin Hajji da Umara, tare da faɗaɗa damar samun ilimin ƙwarewa a wannan fanni.
A wani mataki na nuna kyakkyawar niyya, IsDBI ta bai wa HIN gudummawar ɗaruruwan littattafai da wasu muhimman wallafe-wallafen ilimi, lamarin da zai ƙara bunƙasa ɗakin karatu da albarkatun bincike na cibiyar.
Sauran waɗanda suka halarci taron daga tawagar IsDBI sun haɗa da Mista Sharjeel Ahmad, Babban Kwararre kan Koyarwa ta Yanar Gizo, da Dakta Habeeb Idris Pindiga, Mataimakin Manaja a Sashen Knowledge Horizons.
Wannan ganawa na zama wani muhimmin mataki a ƙoƙarin HIN na amfana da ƙwarewar ƙasashen duniya, ƙarfafa ƙarfin gudanar da bincike da kuma hanzarta sauya tsarin koyar da ilimin Hajji da Umara zuwa tsarin zamani na zamani na dijital a Nijeriya.
Ana sa ran haɗin gwiwar zai taimaka matuƙa wajen ƙara ƙwarewa, inganta ingancin ayyuka da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a harkokin Hajji da Umara a Nijeriya.
