Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya za ta fara aikin zamanantarwa da inganta manyan tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Tin-Can Island da ke jihar Legas a ranar 25 ga Nuwamba, a wani mataki na inganta harkokin gudanar da ayyukan tashoshin da kuma ƙarfafa muhimman ababen more rayuwa na sufuri ta ruwa a ƙasar.
Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Adegboyega Oyetola, ne zai jagoranci bikin aza harsashin fara ayyukan, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Laraba. Mai ba ministan shawara na musamman, Bolaji Akinola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa zamanantar da tashoshin jiragen ruwan biyu, waɗanda suke gudanar da sama da kashi 70 cikin 100 na jigilar kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa ƙasashen waje waɗanda ba na man fetur ba, wani babban mataki ne na ƙoƙarin gwamnatin tarayya na farfaɗo da harkokin sufuri ta ruwa da kuma inganta matsayin Nijeriya a kasuwancin duniya.
Akinola ya bayyana amincewar da aka bayar domin yin cikakken gyara da inganta kayayyakin more rayuwa na tashoshin a matsayin wani muhimmin mataki na tarihi, yana mai cewa tun kusan shekaru 50 da suka gabata ba a taɓa gudanar da aikin zamanantar da su a irin wannan gagarumin mataki ba. Ya ce ayyukan za su magance matsalolin ƙarancin ababen more rayuwa da suka daɗe suna addabar tashoshin, tsofaffin kayayyakin aiki da kuma ƙalubalen gudanar da ayyuka a manyan hanyoyin jigilar kayayyaki da ke kewaye da tashoshin da suka fi aiki a ƙasar.
A cewarsa, ana sa ran aikin zai ƙara ƙarfin tashoshin wajen lodawa da sauke kaya, rage lokacin da jiragen ruwa ke ɗauka kafin su kammala ayyukansu su tashi, da kuma rage tsawon lokacin da kayayyaki ke kwance a tashar kafin a kwashe su. Haka kuma, ya ce aikin zai inganta hanyoyin shiga da fita daga tashoshin, sauƙaƙa jigilar kayayyaki, tare da ƙarfafa matakan tsaro da kiyaye lafiyar ma’aikata da masu amfani da tashoshin.
Ya ƙara da cewa, ayyukan za su samar da ingantaccen yanayin gudanar da harkoki ga masu amfani da tashoshin, masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki a fannin sufuri ta ruwa. Ministan ya bayyana cewa zamanantar da tashoshin jiragen ruwa na Legas wani ɓangare ne na babban shirin gwamnatin tarayya na samar da ingantaccen tsarin tashoshin jiragen ruwa da za su kasance masu haɗin kai a duk faɗin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da zamanantar da wasu manyan tashoshin jiragen ruwa guda huɗu da ke wajen jihar Legas, waɗanda suka haɗa da tashoshin Warri, Onne, Kalaba da Ribas. Oyetola ya ce, “Manufarmu ita ce gina tsarin tashoshin jiragen ruwa na zamani, masu inganci da haɗin kai, waɗanda za su amfani kowane yanki na ƙasar. Duk da cewa tashoshin Apapa da Tin-Can Island suna da muhimmiyar rawa a harkokin kasuwancin Nijeriya da ƙasashen waje, ba za mu iya barin dukkan harkokin sufuri ta ruwa na ƙasar su ta’allaƙa ne a Legas kaɗai ba.”
Ya ce ayyukan da za a gudanar a tashoshin da ke wajen Legas za su ƙara wa aikin zamanantar da Apapa da Tin-Can Island ƙarfi, tare da faɗaɗa ƙarfin Nijeriya wajen lodawa da sauke kayayyaki, da kuma samar da daidaitaccen ci gaban tattalin arziki a sassa daban-daban na ƙasar. Ministan ya kuma danganta wannan shiri da manufar gwamnatin tarayya ta faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, musamman ta hanyar ƙara yawan kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa zuwa ƙasashen waje waɗanda ba na man fetur ba.
Ya ce shirin zai kuma taimaka wajen ƙarfafa masana’antun cikin gida, sauƙaƙa gudanar da harkokin kasuwanci da kuma jawo hankalin masu zuba jari a fannin sufuri ta ruwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, shirin zai inganta haɗin kai tsakanin tashoshin jiragen ruwa, hanyoyin mota da na jirgin ƙasa, hanyoyin sufuri ta cikin ruwa da kuma tashoshin ajiyar kaya na cikin ƙasa, domin samar da ingantaccen tsarin jigilar kayayyaki ta hanyoyi daban-daban. A cewar ma’aikatar, wannan tsari zai sauƙaƙa jigilar kayayyaki daga wuraren da ake samar da su zuwa kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje, rage kuɗaɗen sufuri da kuma ƙara wa kayayyakin da ake ƙerawa a Nijeriya gasa a kasuwannin duniya.
Wannan mataki ya biyo bayan yarjejeniyar bayar da tallafin kuɗi ta fannin fitar da kaya zuwa ƙasashen waje da Nijeriya da Birtaniya suka rattabawa hannu a ranar 19 ga Maris, 2026. A ƙarƙashin yarjejeniyar, ƙasashen biyu sun amince da samar da tallafin kuɗi har fam miliyan 746 na Birtaniya domin zamanantar da tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas da kuma tashar ruwa ta Tin-Can Island.
