An kashe ma’aikacin lantarki bayan yanke wuta kan bashin N300,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ma’aikacin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Benin (BEDC), Oscar Udoka Eze, mai shekaru 38, ya gamu da ajalinsa bayan wasu mutane sun daɓa masa wuƙa, sakamakon katse wa wani kwastoma wutar lantarki bayan an bin sa bashin kusan Naira 300,000 a Jihar Delta.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026, lokacin da marigayin yake gudanar da aikinsa a yankin Idumobi da ke Umunede, cikin yankin da kamfanin ke gudanar da ayyukansa. Sai dai mahukuntan kamfanin BEDC sun buƙaci a tabbatar da an yi wa marigayin adalci, inda suka bayyana kisan nasa a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, tare da yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki kwakkwaran mataki kan waɗanda suka aikata laifin.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, muƙaddashin manajan daraktan kamfanin kuma babban jami’in gudanarwarsa, Jonathan Lawani, ya yi Allah-wadai da kisan tare da buƙatar gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da cewa an hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin. Lawani ya bayyana cewa Eze ya cire wa gida wutar lantarki ne sakamakon bashin da ake bin masu gidan na kusan Naira 300,000, kafin daga bisani mazauna gidan suka bi shi a baya, suka far masa da wuƙaƙe da takubba a wani gida da ke kusa da wurin.

Ya bayyana cewa wannan hari ne aka kai wa ma’aikaci yayin da yake gudanar da aikin da doka ta ba shi izinin yi. Ya jaddada cewa cire wa masu amfani da wutar lantarki layi na ɗaya daga cikin matakan da hukumomin kula da rarraba wutar lantarki suka amince da su domin tilasta biyan kuɗin wutar da aka sha. A kalamansa, “Marigayin bai yi wata gardama da waɗanda suka kai masa harin ba, kuma bai tsokane su ta kowace hanya ba. Aikin da aka tura shi ne kawai yake gudanarwa lokacin da aka kai masa hari.”

Ya kuma bayyana cewa tuni jami’an tsaro suka kama wasu da ake zargi da hannu a kisan. A ƙarshe, Lawani ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Delta da ta gaggauta magance matsalolin tsaron da ke barazana ga ayyukan kamfanin, tare da samar da isasshen kariya ga ma’aikatan wutar lantarki da ke gudanar da ayyukan da doka ta ɗora musu. Ya jaddada muhimmancin samar da yanayin aiki mai aminci ga ma’aikatan kamfanonin rarraba wutar lantarki, waɗanda a kullum suke fita gudanar da ayyukansu domin tabbatar da cewa masu amfani da wutar lantarki suna bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa, musamman wajen biyan kuɗin wutar da suke sha.

By ukarofi

Leave a Reply