Ba a buƙatar rahoton ‘yan sanda kafin duba wanda aka harba – Sufeto-Janar ga asibitoci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sufeto Janar na Rundunar ‘Yan sanda, Olatunji Disu, ya buƙaci asibitoci da jami’an kiwon lafiya a sassan Nijeriya da su riƙa yin magani ga mutanen da aka harba da bindiga ba tare da samun rahoton ‘yan sanda ba kafin kula da su.

Disu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba za su fuskanci hukunci ba kan taimaka wa waɗanda suak jikkata yayin buƙata agajin gaggawa ba, yana mai kira ga al’umma da su riƙa taimaka wa a duk lokacin da aka buƙata. Shugaban ‘yan sandan ya yi wannan kira ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa ta kafar X a ranar Alhamis, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin al’amari.

Ya bayyana cewa, samo rahoton ‘yan sanda ba sharaɗi ba ne wajen yi wa kowaye da ya samu raunukan harbin bindiga magani, yana mai cewa wajibi ne ma’aikatan lafiya su riƙa fifita agajin gaggawa kan jinkirin magani saboda buƙatar sashen gudanarwa.

Musamman Disu ya roƙi likitoci, ungozomomi, da sauran ma’aikatan lafiya da su tabbatar da bai wa masu raunukan harbin bindiga agajin gaggawa.

Kazalika, ya roƙi jama’ar gari da kada su yi ƙasa-a-gwiwa wajen taimakawa ire-iren waɗanda iftila’in ya rutsa da su ta hanyar bayar da agajin gaggawa, yana mai cewa taimakon wanda jikkata ba zai janyo a hukunta su ba.

By Babaji

Leave a Reply