Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Abba Kabir Yusuf yana ɗaya daga cikin amintattun mataimakan siyasa a tafiyar Kwankwasiyya lokacin da ya auri Zainab Musa Kwankwaso a ranar 29 ga Yuli, 2006. Ita kuwa ’ya ce ga ɗaya daga cikin iyalai mafiya ƙarfi a fagen siyasar Jihar Kano. A wancan lokaci, shi yana ƙoƙarin gina matsayinsa a siyasa, yayin da ita ta zaɓi kasancewa a bayan fage, har daga bisani mijinta ya kai matsayin gwamnan Jihar Kano.
Sun gina rayuwar aure tare, inda suka haifi ’ya’ya shida cikin kusan shekaru 20. Mutane da dama sun ɗauka cewa irin wannan aure ba zai taɓa mutuwa ba. Sai dai wannan tunanin ya rushe a wannan makon, a wani zaman shari’a da aka gudanar a Babbar Kotun Yanki ta Mataki na Sama da ke Gudu, Abuja.
Zainab ta bayyana a gaban kotun ba a matsayinta na matar gwamna ba, sai dai a matsayin macen da ke neman ’yancin fita daga auren. A cikin takardar ƙarar da ta shigar, ta bayyana dalilanta a taƙaice, waɗanda suka haɗa da rashin soyayya, rashin kulawa, rashin nuna ƙauna da kuma rashin kyakkyawar alaƙar fahimtar juna a tsakaninsu. Ta bayyana cewa bayan shekaru 20 da zama tare, gidan aurensu ya rasa armashinsa, har ya zama tamkar babu rayuwar aure a cikinsa. Zainab na neman a raba aurensu ta hanyar Khul’i, wata hanya da Shari’ar Musulunci ta tanada wadda mace za ta iya neman rabuwa da mijinta ta hanyar mayar masa da sadakinta, idan ta ga ba za ta iya ci gaba da zama da shi ba.
Wannan hanya ce ta rabuwa da ke ba mace damar fita daga auren cikin mutunci, amma tana ɗauke da babban saƙo: ta gwammace ta mayar da abin da aka ba ta a matsayin sadaki, maimakon ci gaba da zama a auren da ba ta jin daɗinsa. A ranar Talata, Alƙali Ado Muktar ya kira shari’ar domin sauraron ta. A madadin gwamnan, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Sanusi Bature, ya bayyana a gaban kotun.
Ya shaida wa kotun cewa ya karɓi takardun ƙarar, amma har yanzu bai sanar da gwamnan, wanda shi ne wanda ake ƙara, game da batun ba. Saboda haka, ya nemi ƙarin lokaci, inda kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga Disamba. Sai dai makonni kafin wannan zaman kotu, Zainab ta riga ta fice daga gidan gwamnatin Kano, ta koma gidan iyayenta, daga bisani kuma ta tafi Abuja. Don haka, takardar neman saki ta zama sanarwar hukuma kan matakin da tuni ta ɗauka a zuciyarta.
A ranar Litinin ma, Gwamna Abba Kabir Yusuf da kansa ya tabbatar wa magoya bayansa a Kano cewa aurensu ya zo ƙarshe. Cikin raha da ba ta iya ɓoye nauyin lamarin gaba ɗaya ba, gwamnan ya ce daga mata biyu da yake da su, yanzu ya koma da mace ɗaya. Ya kuma nemi addu’ar jama’a domin Allah Ya azurta shi da samun matar da ta dace da shi, tare da bayyana cewa yana farin ciki da matakin da aka ɗauka.
Rikicin siyasa ya taka rawa wajen durƙushewar auren?
Duk da cewa batun ya shafi wani babban jigo a siyasa, akwai wani ɓangare na labarin da ya shafi rayuwar iyali, wanda mutane da dama za su iya fahimta daga irin abubuwan da ke faruwa a gidajen aure.
Wani mutum da ke da kusanci da iyalin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa matsalolin da suka kai ga wannan rabuwa ba sababbi ba ne. A cewarsa, matsalolin sun ƙara tsananta ne bayan lalacewar dangantakar siyasa tsakanin gwamnan da babban jagoransa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda kuma shi ne mahaifin Zainab.
A cewarsa, Zainab ta tsinci kanta cikin wani yanayi mai wuya, inda take jin wasu ’yan siyasa da masu amfani da kafar TikTok suna yi wa mahaifinta ba’a da cin mutunci a cikin gidan gwamnatin mijinta, yayin da take ganin mijin nata ba ya kare martabar mahaifin nata. Majiyar ta ce, “Hakan ya ƙara zama mata abin da ke da wuya ta iya jurewa.”
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba. Haka kuma, takardun shari’ar da aka shigar a kotu ba su ambaci batun siyasa a matsayin dalilin neman sakin ba. Abubuwan da aka bayyana a cikinsu sun ta’allaƙa ne kawai kan rashin soyayya, kulawa da kyakkyawar alaƙar zamantakewa a tsakanin ma’auratan.
Malaman addini da masana sun yi tsokaci kan rabuwar:
Wannan lamari ya sake buɗe ƙofa ga tattaunawa kan matsalolin zamantakewar aure, musamman yadda ma’aurata za su magance saɓani kafin ya kai ga rabuwa. Wasu malaman addini sun tunatar da al’umma irin tanadin da addinin Musulunci ya yi game da sasanta rikicin aure kafin caukar matakin rabuwa.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Inuwa Dutse, Sheikh Awwal Al-Sudais, ya yi ishara da aya ta 128 a cikin Suratun Nisa’i, wadda ta yi bayani kan muhimmancin sulhu da fahimtar juna tsakanin ma’aurata idan aka samu matsala a tsakaninsu. Ya jaddada cewa ya kamata a fara amfani da duk hanyoyin sasanci, ciki har da shiga tsakanin dattawa da sauran masu ruwa da tsaki, kafin a yanke shawarar raba aure, komai girman matsayin iyalan da abin ya shafa.
Shi ma masanin zamantakewar al’umma a Jami’ar Bayero da ke Kano, Dakta Maikano Madaki, ya yi gargaɗin kada a mayar da rushewar aure wani makamin siyasa ko hanyar kai wa wani hari. Ya ce: “Aure abu ne mai tsarki.”
Ra’ayoyin al’ummar Kano kan rabuwar:
A yayin da labarin ke ci gaba da yaɗuwa, wasu mazauna Kano sun bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin, inda suka nuna damuwarsu musamman saboda yadda batun ya shafi iyali mai ’ya’ya shida.
Wata mazauniyar Kano mai suna Habiba Sunusi ta ce: “Duk lokacin da na ga yadda ake cin mutuncin mahaifinta a gabanta, har a gaban mijinta, nakan ji tausayinta. Ni kam ba zan iya jure irin wannan yanayi ba.”
Shi kuwa Yakubu Aminu ya ce: “Saki ba abin farin ciki ba ne, musamman idan aka yi la’akari da cewa akwai yara a cikin auren.”
Wannan lamari ya zama wani tunatarwa cewa mulki da matsayi ba sa kare mutum daga raɗaɗin matsalolin soyayya da zamantakewar aure. Haka kuma, aure da aka shafe shekaru 20 ana ginawa na iya rushewa ba tare da hayaniya ko faɗace-faɗace ba, sai dai a hankali, sakamakon gushewar soyayya da kulawa.
Soyayya, kulawa da fahimtar juna ba abubuwa ne na ƙarin jin daɗi kawai a cikin aure ba; su ne ginshiƙan da ke tabbatar da ɗorewar zaman tare. Idan waɗannan ginshiƙai suka rushe, ko da kuwa gidan aure katafaren gida ne na alfarma, zaman cikinsa kan zama abin da ba za a iya jurewa ba.
Ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Zainab, ranar 15 ga Disamba ce ranar da za a sake sauraron shari’ar. Amma ga ’ya’yansu shida da sauran iyalan da ke bibiyar wannan lamari, babban abin lura shi ne muhimmancin kare soyayya, kulawa da fahimtar juna tun kafin matsaloli su kai ga matakin da ba za a iya gyarawa ba.
