INEC ta amince zaɓen 2023 ya rage kimarta a idon jama’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta amince cewa, babban zaɓen shekarar 2023 ya janyo koma baya ga amincewar jama’a da hukumar, amma ta ce ta yi manyan sauye-sauye a tsarin gudanarwarta domin tabbatar da ingantaccen zaɓe a shekarar 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a Abuja ta bakin Kwamishiniyar ƙasa ta hukumar, May Agbamuche-Mbu, yayin wani taron ƙasa kan zaman lafiya da tsaro da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya. Amupitan ya ce, hukumar ba za ta iya dawo da amincewar jama’a ba tare da amincewa da cewa zaɓen 2023 ya haifar da babban giɓi a wannan fanni ba. Ya ce, “Ba za mu iya ƙarfafa amincewar jama’a ba tare da amincewa da cewa babban zaɓen shekarar 2023 ya haifar da babban giɓi a wannan fanni ba. Sai dai ana samun amincewar jama’a ne ta hanyar aiwatar da ayyuka yadda ya kamata.”

Ya bayyana cewa hukumar ta yi amfani da zaɓukan da ake gudanarwa a tsakanin manyan zaɓukan ƙasa a cikin watanni 13 da suka gabata a matsayin wata dama ta gano kurakurai da matsalolin da ke cikin tsarinta, domin gyara su kafin zaɓen 2027. Ya ce zaɓukan sun haɗa da na gwamnonin jihohin Anambra, Ekiti da Osun, zaɓukan ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja, da kuma zaɓukan cike gurabe guda 16. A cewarsa, hukumar ta samu damar bayyana sakamakon waɗannan zaɓuka cikin sa’o’i 24, lamarin da ya nuna irin ƙoƙarin da take yi na inganta ayyukanta.

Amupitan ya jaddada cewa abin da al’umma ke buƙata daga hukumar zaɓe shi ne sahihin tsarin gudanarwa, gaskiya da kuma bayyana bayanai a fili. Ya ƙara da cewa, INEC ta sake nazarin tsarin ayyukanta bisa tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, inda ta ɓullo da manyan sauye-sauye a fannonin gudanarwa, fasahar zamani da tsarin mulki na cikin gida.

Hukumar ta bayyana muhimman sauye-sauye guda huɗu da take aiwatarwa domin ƙarfafa sahihancin zaɓe da kuma magance matsalolin da aka fuskanta a zaɓukan baya.

1. Tsaftace rajistar masu zaɓe

INEC ta ce ta cire bayanan rajistar masu zaɓe sama da miliyan 1.6 da ba su inganta ba, bayan gudanar da bincike ta amfani da na’urar tantance bayanan masu zaɓe ta hanyar hoton yatsu da fuska (ABIS).

2. Inganta na’urorin tantance masu zaɓe na BVAS

Hukumar ta sayi sabbin na’urorin tantance masu zaɓe guda 57,000, waɗanda ke amfani da hanyoyin tantance bayanan mutum guda biyu. Haka kuma, ta gina wuraren ajiya masu kula da yanayin zafi a sassa daban-daban na ƙasar domin kare na’urorin daga lalacewa sakamakon zafin yanayi. INEC ta kuma rage yawan masu zaɓen da za a riƙa tantancewa da kowace na’urar BVAS daga mutum 1,250 zuwa 850, domin hanzarta tantance masu zaɓe da kuma rage cunkoso a rumfunan zaɓe.

3. Inganta shafin duba sakamakon zaɓe na IReV

INEC ta kuma inganta tsarin fasahar shafinta na tattara da nuna sakamakon zaɓe ta intanet, wanda aka fi sani da IReV. A cewar hukumar, sabon tsarin zai riƙa gano tare da ƙin karɓar sakamakon zaɓe na fom EC8A idan alƙaluman da ke cikinsa ba su yi daidai da lissafi ba ko kuma sun nuna an samu ƙuri’u fiye da adadin masu zaɓen da suka yi rajista a rumfar zaɓen.

4. Gudanar da gwajin zaɓe a faɗin ƙasa

Hukumar INEC ta kuma sanar da cewa za ta gudanar da zaɓen gwaji a facin ƙasar nan a ranar 28 ga Nuwamba, domin gwada ingancin sabbin na’urori da tsarin fasahar da take shirin amfani da su kafin babban zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply