Muna samun sauƙin tsaro a Kankiya – Hakimin Rimaye

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Muna samun sauƙin matsalar tsaro a Ƙaramar hukumar Kankia, muna godiya ga ƙoƙarin da gwamnatin ka ta ke yi, Cewar hakimin Rimaye Alhaji Salim Yusuf Yakubu.

Hakimin ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar ban-girma da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kai fadarsa, a matsayin wani ɓangare na ayyukan rana ta shida na gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko na 2027 a shiyyar Daura.

Ya bayyana cewa lamarin tsaro yana ci gaba da inganta, inda al’ummomi ke komawa harkokin noma.

Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa kan ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen jin daɗin al’umma da gwamnatinsa ke aiwatarwa a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, samar da ruwan sha da shirin bunƙasa al’umma (CDP). Ya kuma yaba kan aikin samar da ruwan sha na Rimaye da gwamna ke yi wanda ya kwashe sama da shekaru 30 ana jira.

By ukarofi

Leave a Reply