Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata fitacciyar ’yar dabarun siyasa kuma mai sharhi kan harkokin kafafen yaɗa labarai daga Amurka, Diana London, ta musanta karɓar dala miliyan 4.5 daga gwamnatin Nijeriya ko wani mutum a ƙasar, bayan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan hirar da ta yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa London, wadda ita ce Babbar Daraktar Kamfanin London Global Strategies, ta ce ta ziyarci Nijeriya ne domin tattaunawa da Tinubu a wani ɓangare na shirin fim ɗin tarihi da take shiryawa, da kuma ganin ƙasar da idonta.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na ɗ ranar Laraba, ta bayyana zargin a matsayin wani yunƙuri na ɓata mata suna, inda ta dage cewa ba gwamnatin Nijeriya ba ce, kuma babu wani mutum a ƙasar da ya biya ta dala miliyan 4.5.
Ta rubuta cewa: “Ina musanta zargin cewa gwamnatin Nijeriya ko wani mutum a Nijeriya ya biya ni dala miliyan 4.5 ba tare da wata shakka ba. Na zo Nijeriya ne domin yin hira da Shugaba Tinubu @officialABAT a wani ɓangare na shirin fim ɗin tarihi, da kuma ganin Nijeriya da idona.
“Wannan yaƙin ɓata suna na iya haifar da hayaniya, amma ba zai sauya gaskiya ko hana ni faɗin gaskiya ba.”
Martanin nata ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar ta bayan hirar da ta yi da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Talata.
Ce-ce-ku-cen ya ƙara ƙamari bayan London ta goge wasu saƙonnin da ta wallafa a baya, inda ta yaba da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka, tare da bayyana Nijeriya a matsayin ƙawarta mafi girma a Afirka.
Daga bisani, ta takaita damar yin tsokaci a shafinta na ɗ, inda ta ƙayyade mutanen da za su iya yin martani ga saƙonninta.
Jaridar ta ruwaito a baya cewa lamarin ya biyo bayan wani rahoto da jaridar Peoples Gazette ta wallafa, wanda ya yi zargin cewa London ta karɓi dala miliyan 4.5 domin gudanar da aikin.
Sai dai bayanan da ke cikin takardun da aka shigar bisa dokar rajistar wakilan ƙasashen waje ta Amurka (Foreign Agents Registration Act), sun nuna cewa Kamfanin London Global Strategies ya karɓi kuɗaɗen da suka kai dala 375,000 daga DCI Group, wani kamfanin masu rajin kare muradun jama’a da ke Amurka, wanda gwamnatin Nijeriya ta ɗauka aiki ta hannun kamfanin lauyoyi na Aster Legal.
An bayyana kuɗaɗen a matsayin kuɗin riƙon kwarya na ayyukan da aka gudanar ƙarƙashin yarjejeniyar aikin rajin kare muradun Nijeriya.
A yanzu London ta fito fili ta musanta karɓar dala miliyan 4.5 daga Nijeriya, inda ta dage cewa ziyararta ƙasar ta kasance ne domin yin hira da shugaban ƙasa a wani shirin fim.
Hirar ta kuma haifar da tambayoyi kan alaƙar aikin kafafen yaɗa labarai da ta gudanar da kuma rawar da kamfaninta ke takawa a yarjejeniyar aikin rajin kare muradun Nijeriya.
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta fitar da kwangilar aikin, bayyana kuɗaɗen da aka biya da takardun biyan kuɗi, tare da wallafa cikakken faifan bidiyon hirar da Tinubu ba tare da an yi masa gyara ko yanke wani ɓangare ba.
Haka kuma, ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta yi ƙarin bayani kan ko hirar tana cikin yarjejeniyar aikin da aka ce an ware dala miliyan 4.5 a kanta.
