Kotu ta ɗaure matashiyar ’yar TikTok bisa zargin cin zarafin Sheikh Daurawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke wa wata matashiya ’yar shekaru 19, Zainab Abubakar, hukuncin ɗaurin watanni biyar a gidan yari tare da bulala 10, ba tare da zaɓin biyan tara ba, bisa zargin cin zarafin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da kuma babban kwamandanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa. An yanke wa Zainab hukuncin ne bayan ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi a gaban kotun, yayin shari’ar da Alƙali Bashir Abdullahi Ibrahim ya jagoranta.

A wani ɓangare na shari’ar, an kuma gurfanar da wasu matasa biyu, Ahmad Usman, wanda aka fi sani da Ortega, mai shekaru 25, da Muhammad Aliyu, mai shekaru 20, bisa zargin haɗa baki da kuma cin zarafin Hukumar Hisbah da babban kwamandanta. Sai dai, ba kamar Zainab ba, waɗannan matasa biyu sun musanta zarge-zargen da ake yi musu.

Bayan lauyoyinsu sun shigar da buƙatar belinsu, kotun ta bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali na tsawon makonni biyu, yayin da take nazarin buƙatar belin da aka gabatar. Haka kuma, alƙalin ya umarci ɓangaren masu gabatar da ƙara da su shirya shaidunsu domin ci gaba da sauraron shari’ar.

By ukarofi

Leave a Reply