Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar sojin Nijeriya ta kare matakin tattaunawa da ta yi da wasu ’yan bindiga masu ɗauke da makamai a Jihar Kwara, inda ta yi watsi da zargin cewa jami’anta sun yi hulɗa ta kusanci da ’yan ta’adda.
Rundunar ta bayyana cewa tattaunawar ta haifar da karɓo bindigogin AK-47 guda 12 da kuma kuɓutar da mutum 10 da aka yi garkuwa da su.
Blueprint Manhaja ta rawaito cewa rundunar haɗin gwiwa ta Operation Savannah Shield ta ce tattaunawar, wadda aka nuna a wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wani ɓangare ne na shirin tsaro da aka ƙaddamar domin kwato makaman da ake riƙe da su ba bisa ƙa’ida ba da kuma kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce bai kamata a ɗauki ganawar da jami’an soji, jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da kuma ’yan bindigar a matsayin gazawar rundunar soji wajen sauke nauyin da ke kanta ba.
Sanarwar, wadda Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji na Rukuni na Tara da Operation Savannah Shield, Laftanar Kanal Ibrahim Shittu, ya sanya wa hannu, ta ce ’yan bindigar sun nuna aniyarsu ta miƙa makamansu da kuma sakin mutanen da suke garkuwa da su.
Shittu ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan ci gaba da kai hare-haren soji da suka matsa wa ’yan bindigar lamba, har ta kai ga ba su da wani zaɓi face su miƙa wuya ko kuma a kawar da su.
Ya bayyana cewa tattaunawar ta haifar da karɓo bindigogin AK-47 guda 12 da kuma kuɓutar da mutum 10 da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta bayyana sakamakon a matsayin shaida kan tasirin dabarun da ba na yaƙi kai tsaye ba, waɗanda ke taimakawa hare-haren soji da ake ci gaba da kai wa ’yan ta’adda da masu fashin daji.
Ta ƙara da cewa dabarun gudanar da ayyukanta sun haɗa da amfani da ƙarfin soji, tattaunawar da bayanan sirri suka jagoranta, da sauran matakan da ba na yaƙi kai tsaye ba domin tunkarar matsalolin tsaron ƙasar.
Rundunar ta bayyana cewa mutanen da suka nuna aniyarsu ta miƙa wuya za su fuskanci tantancewar jami’an tsaro da sauran matakan shari’a da suka dace.
Shittu ya kuma jaddada cewa bai kamata a cutar da mayaƙan da suka miƙa wuya a lokacin da suke miƙa makamansu ba, bisa tanadin dokokin yaƙi, ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da kuma dokokin gudanar da ayyukan soji.
Ya nanata cewa karɓar tuban mutanen da ke ɗauke da makamai wani sahihin mataki ne da doka ta amince da shi a aikin soja, ba wai alamar rashin ƙwarewa ko sassaucin da bai dace ba.
Rundunar ta sake jaddada aniyar rundunar sojin Nijeriya na kare ikon ƙasar da kuma rayuka da dukiyoyin al’ummarta.
Ta buƙaci jama’a da su yi watsi da abin da ta kira fassarar bidiyon da ba ta dace ba, tare da kauce wa yaɗa bayanan da ba a tantance sahihancinsu ba, waɗanda ka iya kawo cikas ga ayyukan tsaro da ake gudanarwa.
Operation Savannah Shield ta tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa za ta ci gaba da sanar da jama’a bayanai kan ayyukanta ta kafafen sadarwa na hukuma.
