Dambarwar auren Gwamna Abba da matarsa, Zainab Kwankwaso

Spread the love

*Kanawa sun bayyana ra’ayoyinsu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Tun bayan jawabin da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2026, a zauren taro na gidan gwamnatin jihar, yayin bikin bayar da tallafin Naira biliyan biyar ga ƙananan ’yan kasuwa, a wani taro da aka gudanar karo na bakwai tun bayan hawansa mulki, jama’a suka fara bayyana ra’ayoyinsu kan kalaman da ya yi game da al’amuran gidansa. Rahotanni sun tabbatar da cewa, rashin fahimta tsakanin gwamnan da mai ɗakinsa, Hajiya Zainab Musa Kwankwaso, ya kai ga shigar da ƙara a kotu, inda take neman a raba aurensu.

A yayin jawabin nasa, gwamnan ya yi kalaman da suka shafi batun sakin aurensu, inda ya ce, idan har batun takardar saki ne, to ya riga ya bayar da ita. Sai dai kalaman nasa sun haifar da muhawara a tsakanin malamai, inda wasu suka bayyana cewa sakin ya tabbata, yayin da wasu kuma ke ganin cewa bai yiwu ba. Hakan ya nuna bambancin fahimta kan batun a tsakanin malamai.

Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa, batun sakin aurensa ya rage masa matsayi daga kofur zuwa kwanstable. Ya kuma umarci Kwamishinansa, Bature Dawakin Tofa, da ya yi abin da ya dace wajen cike gurbin da ya dace, yana mai cewa ƙofa a buɗe take domin cike gurbin da wadda ta dace, domin ba zai ci gaba da zama da mace guda ɗaya ba.

A jawabi biyo hakan, Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa, kalaman da Gwamna Abba ya yi sun tabbatar da saki kan matarsa, Zainab, saboda ya yi su ne a cikin nishaɗi.

Wannan kalami na gwamna ya jawo martani daga wasu al’ummar Kano, inda da dama suka bayyana ra’ayoyinsu kan abin da ya faru, kamar haka:

Walwala da jin daɗi ba sa sa mace ta nemi a sake ta – Baba Imposable

Masanin al’adu da addini, Dakta Tahir Adamu, wanda aka fi sani da Baba Imposable, ya ce, walwala da jin daɗi ba sa zama dalilin da zai sa mace ta nemi a sake ta, duk da cewa saki ba haramun ba ne, kuma ana yin sa a gidajen malamai, sarakuna da talakawa. Sai dai ya ce yadda lamarin ya faru a wannan karon ya saɓa wa ƙa’idojin al’ada, addini da mutunci, tare da taɓa martabar Kano. Ya ce yanzu wasu daga wurare daban-daban sun fara yi wa Kano gori, har ma ana haɗa maganar wani malami da ya rasu a Bauchi da kalaman gwamnan kan saki, inda ake cewa komai dai Kano.

Dakta Baba Imposable ya ce a matsayinsa na dattijo da gwamnan ya sani, wanda ya taɓa ziyartarsa har gida, kuma yake cikin Kwamitin Dattawan Kano, da yana da damar ganinsa, da ya ba shi shawarar kada ya ɗauki wannan mataki. Ya ƙara da cewa, masu ƙarfafa gwamnan kan wannan lamari da kashi 90 cikin 100 ba masoyansa ba ne. Ya ce bai kamata Kano ta kai ga wannan matsayi ba, musamman idan aka yi la’akari da cewa ma’auratan sun shafe shekara 20 tare. A cewarsa, abin da ya kamata gwamnan ya yi, idan har yana son a raba auren, shine ya tura lauyansa kotu domin aiwatar da abin da yake so, ba sai an yi irin waɗannan kalamai a bainar jama’a ba.

Dakta Baba Imposable, wanda dattijo ne, ɗan siyasa, masanin al’ada da addini, kuma malamin jami’a, ya bayyana waɗannan ra’ayoyi ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon Lumana International a ranar Talatar da ta gabata.

Wannan magana ta sa na kwana cikin alhini da baƙin ciki – Hajiya Khadija Shuaibu

Hajiya Khadija Shuaibu, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin mata a Kano, ta ce kalaman gwamnan sun sa ta shiga cikin alhini da baƙin ciki. Ta bayyana cewa ita ba ’yar siyasa ba ce, amma tana ƙaunar Gwamna Abba. Ta ce tun a shekarar 2019 ta fito ta kaɗa masa ƙuri’a, duk da cewa tana cikin mata da aka raba wa kayan abinci da shinkafa domin su ƙi zaɓensa. Ta ce a lokacin zaɓen 2023 ma, an raba wa mata taliyar da sauran kayan abinci da sharadin cewa duk wadda ta karɓa za ta zaɓi wanda ya ba ta kayan.

Hajiya Khadija ta bayyana cewa tana cikin matan da suka hana wani mutum shiga wani wuri har sai jami’an tsaro suka zo suka tafi da shi, saboda goyon bayan da suke yi wa gwamnan. Sai dai ta ce wannan batu ya girgiza ta, musamman kasancewar ita da sauran matan suna da ’ya’ya mata da maza. Ta ƙara da cewa da dama daga cikin matan sun kwana cikin alhini da damuwa, kuma har yanzu lamarin yana damunsu. Ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani ɗan siyasa da zai sake yin irin wannan abu, za su nuna masa rashin amincewarsu. Hajiya Khadija ta bayyana waɗannan ra’ayoyi ne kan abin da ya faru tsakanin gwamnan da mai ɗakinsa.

Ya kamata dattawa da malamai su shiga tsakani – Malam Ahmad Rimin Gado

Malam Ahmad Rimin Gado, wani matashin ɗan kasuwa a Kano, ya ce abin da ya faru ya ba shi mamaki, musamman idan aka yi la’akari da matsayin gwamna. Ya ce abin da ya kamata shi ne gwamnan ya zauna da dattawa da sauran jagororin al’umma, musamman waɗanda ya taɓa faɗa da su a baya, domin tattauna lamarin cikin hikima. Ya ce ma’auratan sun shafe shekara 20 tare, ba kwana 20 ba, kuma Allah ya albarkace su da zuriya. Ya ƙara da cewa duk matakin da mutum zai ɗauka, ya kamata ya kasance mai haƙuri.

Malam Ahmad ya ce ɗan Adam yana da ’yancin kai ƙara kotu, haka nan mata ma suna da wannan ’yanci. Sai dai a matsayinsa na mai ba da shawara, ya buƙaci gwamnan da ya yi haƙuri, tare da ba wa dattawa da sauran masu ruwa da tsaki damar shiga tsakani, domin lamarin ya shafi al’ada da addinin Kano.

Gwamnan Kano ba shi da laifi – Malam Safiyanu Yunusa

Malam Safiyanu Yunusa, mai sana’ar takalma, ya ce bai ga laifin Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ba kan abin da ya faɗa. Ya bayyana cewa maigida shi ne jagoran gida, kuma tunda matar ta zaɓi a sake ta har ta kai ƙara kotu, bai ga laifin gwamnan ba idan ya yi magana a kan batun sakin a taron jama’a.

A cewarsa, kotu ma idon duniya ce, kuma duk abin da ya kai kotu yana iya shiga jarida, rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai. Saboda haka, ya tambayi dalilin da zai sa a ɗora wa gwamnan laifi kan yin magana a kan batun.

’Ya’ya shida ba ƙaramin abu ba ne – Alhaji Lawan ƙofar Nassarawa

Alhaji Lawan ƙofar Nassarawa Bakin ƙofa ya ce gwamna mutum ne mai babban matsayi da Allah Ya ɗaukaka, don haka dole ne ya yi haƙuri da wasu abubuwan da ba ya tsammani. Ya ce mulki ba a yin sa don jin daɗi kawai, sai dai don kishin ƙasa, bautar al’umma da tabbatar da adalci, domin mutum ya samu dacewa a ranar Alƙiyama.

Ya ƙara da cewa ya’yan shida ba ƙaramin abu ba ne, don haka ya kamata a yi haƙuri da abin da ya faru, domin a bar wa ’yan baya abin koyi. Ya kuma yi nuni da cewa ana kallon Kano a matsayin abin koyi, musamman ganin yadda aka fara aurar da zawarawa a Hukumar Hisbah, kuma Gwamna Abba ya yi irin wannan aure, har ma ya mayar da shi auren gata da ya haɗa ’yan mata da zawarawa. Ya ce bai kamata a so wasu su yi koyi da irin wannan lamari ba, balle ma idan gwamna ne ya aikata shi.

“Da ni ne gwamna, da ba zan bayyana batun sakin ba”

Wani mutum da ya ƙi a ambaci sunansa ya ce, da shi ne gwamna, ko da matarsa ta kai shi kotu, ba zai bayyana batun sakin a bainar jama’a ba. Ya ce zai jira shari’a ta kammala tare da yanke hukunci, domin alkalai mutane ne masu daraja, basira da hangen nesa.

“Ya kamata mutum ya yi la’akari da al’ada da addininsa”

Malam Lawan Abdullahi Fanta da Malam Muhammad I. Safiyanu sun bayyana cewa duk abin da mutum ya ɗauka, ko ya yi ko bai yi ba, ya kamata ya yi la’akari da yadda hakan zai shafi al’ummarsa, makwabtansa, ’yan uwansa, al’adarsa da addininsa, domin kauce wa nadama.

Wannan lamari ya ba mu tsoro – Hajiya Fa’iza Adamu

Hajiya Fa’iza Adamu, wata matashiya da take addu’ar ganin ranar aurenta cikin ƙoshin lafiya da yalwa ga mijinta da al’umma baki ɗaya, ta ce lamarin ya ba su tsoro. Ta yi addu’ar Allah Ya sa kada su ji irin wannan labari ko su ga irin faruwar hakan, tare da roƙon Allah Ya kiyaye su daga duk abin da ba ya cikin adalci.

Ya kamata namiji ya yi haƙuri da iyalinsa – Hajiya Madina Ado

Hajiya Madina Ado ta ce idan har gaskiya ne an yi wa mai girma gwamna irin wannan abu a aurensa da Hajiya Zainab, wadda ta kasance tare da shi kafin Allah Ya kai shi wannan matsayi, to lamarin abin mamaki ne. Ta ce abin da ya fi dacewa shi ne namiji ya yi haƙuri da iyalinsa, haka kuma mace ta kasance mai biyayya ga mijinta bisa tsarin addini da kyawawan al’adunsu.

Ya kamata a warware matsala a gida kafin ta kai kotu – Alhaji Abdulhadi

Malam Alhaji Abdulhadi, wani ƙwararren malamin makaranta kuma masani kan al’adu da al’amuran yau da kullum, ya ce abin da aka sani shi ne kafin mace ta kai ƙarar mijinta kotu domin a raba aure, ya kamata ta fara sanar da shi a gida. Ya ce a nan ne ya kamata a fara tattauna matsalar domin neman mafita, kafin ta kai ga matakin da zai sa duniya ta ji labarin abin da ke faruwa a tsakaninsu.

By ukarofi

Leave a Reply