Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An gudanar da bikin cikar makarantar sakandaren Dawakin Kudu, wadda a yanzu ta koma makarantar kimiyya da fasaha, shekara 50 da kafuwa, wato daga shekarar 1975 zuwa 2025.
An gudanar da taron ne a ranar Asabar da ta gabata a ɗakin taro na makarantar.
Da yake yi wa manema labarai ƙarin bayani kan dalilin shirya taron, Jami’in Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar tsofaffin ɗaliban ajin shekarar 1975, Malam Muhammad Ali Abdullahi, ya ce sun shirya taron ne domin sake haɗuwa da juna da ƙarfafa zumunci bayan shafe sama da shekaru 45 ba tare da sun haɗu ba.
Ya bayyana cewa tun farko makarantar sakandare ce, kafin juyin mulkin Janar Murtala Muhammad, lokacin da Gwamnan Kano na wancan lokaci, Kanar Sani Bello, ya mayar da ita makarantar kimiyya da fasaha, lamarin da ya haifar da raba ɗaliban zuwa makarantu daban-daban.
A cewarsa, a lokacin ne aka buɗe makarantu biyu, ɗaya a Dawakin Tofa, ɗayan kuma a Dawakin Kudu.
Ya ƙara da cewa an kafa ƙungiyar ne domin taimaka wa ɗaliban da makarantar ta yaye, da kuma duba matsalolin da ke addabar makarantar domin nemo hanyoyin magance su, tare da inganta harkokin koyarwa da koyo da jin daɗin ɗalibai.
A nasa jawabin, shugaban taron kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya taya mambobin ƙungiyar murnar ganin wannan lokaci, yana mai cewa ba abin mamaki ba ne ganin yadda lokaci ke saurin wucewa.
Ya ce shirya irin wannan taro abu ne mai kyau kuma an yi shi a lokacin da ya dace, domin yana ba tsofaffin ɗalibai damar tuna abubuwan da suka yi tare a lokacin da suke karatu, inda suke cin abinci da kwana a wuri guda, duk da cewa sun fito daga wurare daban-daban.
Shekarau ya kuma yaba wa wanda ya kafa makarantar, yana mai cewa kafa irin waɗannan makarantu na buƙatar hangen nesa, domin zuba jari a harkar ilimi ba abu ne da ake ganin ribarsa nan take ba, kamar yadda ake samu a wasu fannoni, sai dai yana ɗaukar lokaci kafin a ga tasirinsa.
Ya ce ilimi yana gyara tunanin al’umma tare da samar da nagartattun ‘yan ƙasa masu amfani ga ƙasa.
A nasu jawaban, wakilan Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Kwamishinan Jinƙai, Alhaji Muktar Ishak, ya wakilta, da na Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Farfesa Isa Chamo, ya wakilta, sun bayyana taron a matsayin abin a yaba.
Sun jaddada muhimmancin kafa ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, suna mai cewa ta hanyar irin waɗannan ƙungiyoyi ne ake samun damar magance wasu matsalolin makarantu.
Sun kuma bayyana cewa manyan injiniyoyi, likitoci da sauran ƙwararrun mutane da ake alfahari da su a jihohin Kano da Jigawa, sun fito ne daga makarantu irin waɗannan.
Mahalarta taron sun yi kira ga ɗaliban makarantar da su mayar da hankali kan karatunsu, suna masu cewa wata rana su ma za su iya zama manyan mutane a irin waɗannan wurare. Sun bukace su da ƙoƙari domin samun sakamako mai kyau da za a yi alfahari da shi a nan gaba.
A yayin taron, an kafa wata ƙungiya mai suna Endowment Fund, domin tallafa wa ɗaliban da suka yi fice a karatu amma ba su da halin ci gaba da karatu, ta hanyar biyan musu kuɗin makaranta, tare da samar da kayan aiki ga makarantar.
Taron ya samu halartar wakilin wanda ya kafa makarantar, tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, wakilan gwamnonin Kano da Jigawa, Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Shugaban ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu, Hon. Sani Ahmad Mai Rago, Hakimin Dawakin Kudu kuma ɗan Makwayon Kano, Alhaji Abba Yusuf, da sauran manyan baƙi.
