Daga GAMBO ISA a Abuja
Mai Martaba Sarkin Giade, Alhaji Muhammad Sabo Abdulkadir, ya yaba wa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, bisa ayyukan ci gaba da yake samar wa al’ummar jihar, da kuma ƙirƙiro sabbin masarautu domin inganta harkokin mulki da ci gaban al’umma.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake nuna godiyarsa ga Gwamna Bala Muhammad bisa karrama shi da sarautar Magajin Garin Giade. Ya ce wannan karramawa ta nuna yadda gwamnan ke girmama gudummawar da al’ummomi da masarautu ke bayarwa wajen ci gaban jihar.
Mai Martaba Sarkin Giade ya ce ƙasar Giade tana da dogon tarihin da ya shafi Daular Usmaniyya, inda ya bayyana cewa shi ne Sarkin Yanka na farko a Masarautar Giade. Ya gode wa gwamnan bisa wannan karramawa da kuma ƙoƙarin da yake yi na samar da sabbin masarautu da bai wa al’ummomi guraben da suka dace da matsayinsu da tarihinsu.
Haka kuma, Sarkin ya bayyana cewa Gwamna Bala Muhammad ya kawo gagarumin ci gaba a fannoni daban-daban, wanda ya taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar Jihar Bauchi, musamman ma al’ummar ƙasar Giade.
Ya ce gwamnan ya inganta wasu haƙƙoƙin al’ummar Giade, saboda haka babu abin da za su ce masa face godiya da yi masa fatan alheri.
Mai Martaba Sarkin ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da fatan alheri, tare da kasancewa masu kyawawan ɗabi’u da tarbiyya a kodayaushe.
Haka zalika, ya yi kira ga hakimai da sauran masu riƙe da muƙaman gargajiya da su ci gaba da kiyaye mutuncin al’umma, gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, tausayi da adalci.
