Yadda jihohin Arewa suka yi zarra a aiwatar da manufofin kiwon lafiya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jihohin Arewacin Nijeriya sun zama kan gaba wajen aiwatar da manufofi, shawarwari da kuma ƙudirorin Majalisar ƙasa kan Kiwon Lafiya (NCH), inda yankin Arewa ta Tsakiya ya samu maki mafi yawa da kashi 67.1 cikin 100, sai Arewa maso Yamma da kashi 64.3 cikin 100.

Rahoton matsayi na jihohin, wanda aka fitar yayin taron majalisar karo na 67 da aka gudanar a Jihar Nasarawa, ya kuma nuna cewa Jihar Neja ce ta zo ta farko a duk faɗin ƙasar da maki kashi 90 cikin 100, yayin da Jihar Bayelsa ta kasance a matsayi na ƙarshe da kashi 22 cikin 100. Bayanan sun nuna cewa yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma sun zarce matsakaicin makin ƙasa baki ɗaya, wanda ya tsaya a kashi 55 cikin 100. A gefe guda kuma, Kudu maso Yamma ta samu kashi 48.5, yayin da Kudu maso Kudu ta samu kashi 45 cikin 100.

A matakin jihohi, Neja ce ta zama jiha mafi ƙwazo cikin jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja. Jihar Binuwai ta zo ta biyu da kashi 85 cikin 100, sai Akwa Ibom da kashi 83, Abia da kashi 81, sannan Kogi da kashi 79 cikin 100.

Haka kuma, jihohin Arewa guda bakwai sun samu shiga cikin jihohi 10 da suka fi ƙwazo wajen aiwatar da shawarwarin majalisar, wadda ita ce mafi girman hukumar da ke tsara manufofin kiwon lafiya a Nijeriya.

An gabatar da wannan ƙididdiga ne yayin zaman ƙwararru na taron Majalisar ƙasa kan Kiwon Lafiya karo na 67, wanda aka gudanar a Jihar Nasarawa ranar 16 ga Nuwamba, 2026. Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Neja, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya, Dakta Murtala Muhammad Bagana, ta danganta wannan nasara da aiwatar da sabon shirin inganta kiwon lafiya na Gwamna Mohammed Umaru Bago, wanda aka fi sani da New Niger Health Agenda.

Da yake tabbatar da sakamakon ƙididdigar, Bagana ya ce ma’aikatar ta samar da jagorancin ƙwararru da kuma ingantaccen tsarin gudanarwa da haɗa ayyuka, domin mayar da hangen nesan gwamnan na bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya zuwa manufofi, shirye-shirye da ayyukan da ake aiwatarwa a zahiri. Ya bayyana cewa gyare-gyaren sun fi mayar da hankali ne kan ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko, gyarawa da inganta cibiyoyin kiwon lafiya, samar da muhimman kayan aikin jinya, horaswa da bunƙasa ma’aikatan lafiya, da kuma inganta ƙarfin hukumomin da ke kula da harkokin kiwon lafiya.

A cewarsa, an tsara waɗannan shirye-shirye ne domin mayar da kiwon lafiya wani muhimmin ginshiƙi na bunƙasa ƙwarewar al’umma, tare da tabbatar da cewa mazauna jihar sun samu damar yin amfani da ingantattun ayyukan kiwon lafiya cikin sauƙi da araha. Kwamishinan ya ce samun maki kashi 90 cikin 100 ya tabbatar da muhimmancin daidaita manufofi yadda ya kamata, jajircewar hukumomi wajen gudanar da ayyukansu da kuma sa ido akai-akai, wajen samar da ingantaccen sauyi a harkokin kiwon lafiya.

Ya ƙara da cewa, “Wannan nasara ta kuma nuna ƙudirin ma’aikatar na wuce matakin tsara manufofi kawai, zuwa ga aiwatar da shawarwari da ƙudurorin da aka cimma a taron Majalisar ƙasa kan Kiwon Lafiya. Duk da haka, wannan nasara ta ƙara ɗora wa ma’aikatar nauyin ci gaba da wannan ƙoƙari, magance matsalolin da har yanzu suke akwai, tare da zurfafa gyare-gyaren da ake gudanarwa a dukkan sassan tsarin kiwon lafiyar jihar.”

By ukarofi

Leave a Reply