Majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da dokar kafa ’yan sandan jihohi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dokoki ta ƙasa ta ce an kammala dukkan matakan amincewa da kudirin sauya kundin tsarin mulki, wanda yanzu ya shirya domin miƙawa Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu.

Dukkan majalisun dokokin jihohi 36 na Nijeriya sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa rundunonin ’yan sandan jihohi, lamarin da ya share fagen miƙa kudirin ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya sanya masa hannu.

Magatakardar Majalisar Dokoki ta ƙasa, Kamoru Ogunlana, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana amincewar a matsayin kashi 100 cikin 100 na majalisun dokokin jihohin ƙasar.

Wannan amincewa ta wuce adadin majalisun dokokin jihohi 24 da kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, kamar yadda aka yi masa gyara, ya tanada a ƙarƙashin sashe na 9(2).

Ogunlana ya ce: “Magatakardar Majalisar Dokoki ta ƙasa na sanar da cewa dukkan majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da kudirin dokar sauya kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 domin samar da rundunonin ’yan sandan jihohi da sauran abubuwan da suka shafi hakan.

“Wannan ya nuna cewa kashi 100 cikin 100 na majalisun dokokin jihohin sun amince da kudirin, wanda ya wuce adadin majalisu 24 da sashe na 9(2) na kundin tsarin mulki ya tanada.”

Wannan mataki ya nuna kammala aikin tantancewa da nazarin kudirin da majalisun dokokin jihohi suka gudanar, bayan shafe makonni suna tattaunawa kan batun kafa ’yan sandan jihohi.

A ranar 3 ga Nuwamba, Majalisar Dokoki ta ƙasa ta sanar da cewa majalisun dokokin jihohi 28 sun riga sun amince da kudirin, adadin da ya wuce kason kashi biyu bisa uku da ake buƙata.

A lokacin, magatakardar ya bayyana cewa za a ci gaba da karɓar amincewar sauran jihohin kafin a miƙa kudirin ga shugaban ƙasa.

Washegari, Majalisar Dattawa ta bai wa sauran majalisun dokokin jihohi shida wa’adin zuwa ranar 15 ga Nuwamba domin su sanar da matsayarsu, bayan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa jihohi 30 sun amince da kudirin.

A cikin sabuwar sanarwar, Ogunlana ya bayyana cewa duk da cewa kudirin ya riga ya cika sharuddan kundin tsarin mulki da na gudanarwa da ake buƙata domin miƙa shi, shugabannin Majalisar Dokoki ta ƙasa sun ɗan jinkirta miƙa shi ne domin ba da damar yin ƙarin shawarwari da cimma matsaya tsakanin jihohin ƙasar.

Ya ce: “Yana da muhimmanci a lura cewa kudirin ya daɗe da cika dukkan sharuddan kundin tsarin mulki da na gudanarwa da ake buƙata domin miƙa shi, kamar yadda kundin tsarin mulki da Dokar Tabbatar da Ingancin Dokoki ta shekarar 2004 suka tanada.

“Amma shugabannin Majalisar Dokoki ta ƙasa sun bayar da umarnin ɗan jinkirta miƙa kudirin domin ba da damar samun cikakkiyar matsaya ta ƙasa da kuma shigar da dukkan jihohin tarayyar cikin shawarwarin.”

Ya bayyana amincewar da dukkan majalisun suka yi a matsayin wani sabon tarihi na haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin matakan gwamnati daban-daban.

Ogunlana ya ƙara da cewa: “Amincewar da aka samu baki ɗaya da kudirin wata babbar shaida ce ta haɗin gwiwa tsakanin Majalisar Dokoki ta ƙasa da majalisun dokokin jihohi, da kuma kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin ɓangarorin zartarwa na gwamnatin tarayya da na jihohi.”

Magatakardar ya kuma ce ofishinsa ya kammala aikin tantancewa, don haka kudirin ya shirya domin miƙa shi ga Shugaban ƙasa domin sanya masa hannu.

Ya ce: “Bayan kammala aikin tantancewa da ofishina ya gudanar, yanzu kudirin ya shirya domin miƙa shi ga Shugaban ƙasar Tarayyar Nijeriya domin ya sanya masa hannu.”

Ogunlana ya bayyana cewa wannan nasara za ta zama ginshiƙi ga Majalisar Dokoki ta ƙasa wajen kammala wasu kudirorin gyaran kundin tsarin mulki da ake shirin miƙawa majalisun dokokin jihohi.

Ya ce wannan ci gaba zai taimaka wa Majalisar Dokoki ta ƙasa wajen kammalawa da miƙa sauran kudirorin gyaran kundin tsarin mulki na zagaye na shida ga majalisun dokokin jihohi domin su nazarce su da wuri.

Tun da farko, Majalisar Dokoki ta ƙasa ta miƙa kudirin kafa ’yan sandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi 36 domin su yi nazari a kansa, a matsayin wani ɓangare na aikin bitar kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.

ƙudirin na neman samar da sahihin tushe a kundin tsarin mulki domin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi, waɗanda za su yi aiki tare da rundunar ’yan sandan tarayya da ake da ita.

A ƙarshe, Magatakardar ya yaba wa gwamnonin jihohi 36, shugabannin majalisun dokokin jihohi da mambobinsu, da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da gudunmawar da suka bayar wajen cimma wannan matsaya.

By ukarofi

Leave a Reply