Rikicin CAN a Nasarawa: Ba ni nake jawowa ba – Rev. Abari

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Shugaban riƙo na ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Nasarawa, Rev. Dr. Kefas Abari yayi bayani kan rikicin shugabanci dake addabar reshen ƙungiyar a jihar inda ya ƙaryata zargin cewa shi ne ya shirya dakatar da zaɓen sabuwar majalisar zartarwa da aka so a gudanar kwanakin baya a Lafia.

Rev. Abari wanda ya yi bayanin a wata hira ta musamman da wakilinmu a Lafia ya bayyana zargin wanda ake dangantawa ga ɗaya daga cikin ɓangarorin ƙungiyar a jihar, a matsayin ƙarya, ɓatagari kuma mai iya ƙara rura wutar rabuwa a tsakanin kiristoci a jihar.

A cewarsa saɓanin ikirarin da ake yaɗawa ba a dakatar da zaɓen ba ko kuma aka lalata shi da tashin hankali ba amma taron ya kasance cikin lumana da natsuwa kafin shiga tsakani da ƙungiyar ta ƙasa ta yi.

Ya bayyana cewa wakilai sun riga sun taru kuma shirye-shirye sun yi nisa don fara zaɓen sai nan take ya samu umarni daga sakatariyar ƙasa ta CAN da ke Abuja, tana umurtar a dakatar da aikin na wucin gadi.

Shugaban riƙon yace hukumar ƙasar ta ɗauki matakin ne domin ta samu damar warware wasu matsalolin cikin gida da ke shafar reshen jihar, yana mai jaddada cewa dakatarwar ba shawararsa ta kansa ba ce kuma ba a yi ta don cutar da wani mutum ko ɓangare ba.

Rev. Abari ya tabbatar cewa ba shi da wani muradun kansa na tsawaita zamansa a ofis, yana mai lura cewa aikin da aka ba wa majalisar zartarwa ta riƙo a bayyane yake: shirya zaɓe mai inganci, ‘yanci da adalci wanda zai samar da shugabanci da kowa zai amince da shi ga ƙungiyar a jihar.

Ya tabbatar wa mambobi cewa da zarar hukumar ƙasar ta kammala shiga tsakaninta tare da warware matsalolin da ke tafe, za a sanar da sabuwar ranar kuma za a gudanar da zaɓen ba tare da wani jinkiri ba.

Shugaban riƙon na CAN ya kuma yi kira na musamman ga ɓangarori daban-daban dake ƙunshe da ƙungiyar a jihar su guji zargi da hamayya yana mai gargaɗin cewa rashin haɗin kai zai raunana murya ɗaya ta coci a jihar.

Ya yi kira ga Kiristoci a faɗin Jihar Nasarawa baki ɗaya  da su cigaba da zama kansu a haɗe su kuma zama masu kula da junan su kamar ‘yan’uwa maza da mata, kuma su nuna kauna ga juna a kowane lokaci da kuma duk inda suka sami kansu ba tare da la’akari da ikilisiya ko ɓangare ba.

A ƙarshe sai Rev. Abari ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa za a warware wannan matsala nan ba da jimawa ba, yana mai cewa shugabancin riƙon CAN din a jihar zai cigaba da jajircewa wajen bayyana gaskiya da adalci da hada kowa don mika ragama ga sabbin shugabannin ƙungiyar a jihar da aka zaɓa a kowanne lokaci bisa ƙa’ida wadda za ta samu amincewar dukkan Kiristoci a Jihar Nasarawa.

By ukarofi

Leave a Reply