
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsarom Nijeriya DHQ, ta ƙaryata kai kakin sojoji ga ‘yan bindiga a wani faifan bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, wanda ke nuna ‘yan bindiga tare da wasu tarin kakin soja. Bidiyon ya nuna cikin daji da kakin sojoji da aka baza su a ƙasa, yayin da aka ga wasu kuma cikin buhuna.
Da yake tsokaci kan al’amarin, Darakta yaɗa labaran hedikwatar, Manjo-Janar Michael Onoja, ya ce ba ya yadda za a yi a ce an samo waɗannan kaya daga wajen sojojin Nijeriya. Ya kuma yi watsi da cewa ta yiwu an samu kayan ne bayan ‘yan bindiga sun farmaki motar da ke jigilarsu, inda ya ce ba su samu wannan rahoton ba.
Bidiyon ya nuna kakin soja kala biyu – na daji da wanda ake amfani da shi a sahara, a hannun ‘yan bindigar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka jima ana nuna damuwa akan amfani da kakin sojoji ta haramtacciyar hanya daga ɓangaren fararen hula da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a Nijeriya.
A watan Fabarairun 2024 ne Gwamnatin Tarayya ta jaddada taƙaice amfani da kakin soja ga waɗanda ba jami’ai ba biyo bayan nuna damuwa kan yadda ‘yan ta’adda suke amfani da su wajen yin basaja a matsayin sojoji don aikata miyagun laifuka.
