Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban kamfanin baƙin mai na Abe, Alhaji Isa Balarabe, wanda aka fi sani da Abe, ya yi kira ga gwamnati da ta rage harajin da ake karɓa daga ’yan kasuwa, tare da ƙarfafa wa matasa gwiwa ta hanyar tallafa musu domin su dogara da kansu.
Alhaji Abe ya yi wannan kiran ne a yayin bikin buɗe sabon babban ofishin kamfanin Abe Lubricant da ke ƙofar Waika, inda ya bayyana farin cikinsa tare da gode wa Allah bisa damar da Ya ba su ta buɗe ofishin.
Ya ce kamfanin ya fara ne tun yana ɗan ƙarami, inda ya riƙa bunƙasa a hankali, har cikin yardar Allah ya haɓaka saboda suna kawo baƙin mai mai inganci da sauƙin farashi, wanda hakan ya kai shi matsayin da yake a yau.
Ya ce tun kafin buɗe wannan sabon ofishi, suna da aƙalla ma’aikata 78 da suke aiki tare da su, wanda hakan wani ƙoƙari ne na tallafa wa matasa ta hanyar samar musu da aikin yi.
Abe ya ce duk wanda yake kasuwanci ya san irin raɗaɗin da yawan haraji ke jawowa. Ya bayyana cewa ya kamata gwamnati, ko da ba za ta janye harajin gaba ɗaya ba, ta rage kaso mai yawa daga abin da ake karɓa, domin hakan zai taimaka wa masu harkokin kasuwanci wajen samun damar ɗaukar matasa su koya musu sana’a.
Ya ce kamar yadda kowace irin sana’a ke da nata ƙalubalen, haka su ma suke da nasu, domin kowa ya san halin da ƙasar nan ke ciki na tashin farashin kayayyaki, wanda shi ne babban ƙalubalen da suka fi fuskanta a kasuwancinsu na baƙin mai.
Ya yi nuni da cewa mutum zai sayo kaya, ya sayar, amma idan ya tashi sake sayo kaya, sai ya ƙara samo wasu kuɗaɗe domin cike gibin da aka samu, saboda farashin ya ƙaru fiye da yadda ya sayar a baya.
Ya ce suna ƙoƙarin ganin sun sauƙaƙa wa mutane farashi domin ƙarfafa musu gwiwa, musamman masu tuƙa Adaidaita Sahu da masu babura masu ƙafa biyu, inda suke sauƙaƙa musu farashi domin su gudanar da harkokinsu cikin sauƙi.
Shi ma da yake zantawa da ’yan jarida, Alhaji Abubakar Ghali Rabiu ya ce suna farin ciki da alfahari bisa buɗe wannan ofishin na baƙin mai da ɗansu, maƙocinsu kuma uba a gare su, Alhaji Abe, ya yi.
Ya ce buɗe ofishin ya samar da damar da wasu za su samu aikin yi, wanda hakan zai taimaka wajen rage rashin aikin yi, da kuma rage wa gwamnati nauyi tare da bunƙasa kasuwanci.
Ya yi kira ga abokan hulɗa da kamfanin Abe da cewa akwai kulawa sosai da girmama abokan hulɗa a kamfanin, inda ake sayar da baƙin mai mai inganci da sauran kayayyaki, kuma abokan hulɗa na jin daɗin mu’amalarsu da kamfanin.
Abubakar Ghali Rabiu ya ce samar da irin waɗannan wuraren sana’o’i zai taimaka wajen rage rashin aikin yi, domin idan ana buɗe irin waɗannan wurare, matasa za su samu ayyukan yi. Saboda haka, ya buƙaci ’yan kasuwa da su ƙara buɗe irin waɗannan wurare a sassa daban-daban.
