Tinubu zai fitar da ’yan Nijeriya miliyan 80 daga talauci ƙarƙashin shirin tallafin Dala miliyan 500

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta fitar da ’yan Nijeriya tsakanin miliyan 50 zuwa miliyan 80 daga ƙangin talauci, ta hanyar faɗaɗa shirin farfaɗo da tattalin arziki da tallafa wa al’umma na Nijeriya (NG-CARES), bayan samun nasarar matakin farko na shirin, wanda ya taimaka wajen fitar da mutane miliyan 17 daga talauci.

Ma’aikatar Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki ta bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin wani taron fasaha na shirin ƙarin tallafin kuɗi na NG-CARES.

Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Bagudu, ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin kare ’yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi daga illolin sauye-sauyen tattalin arziki da kuma matsalolin da ka iya tasowa sakamakon sauyin yanayin tattalin arziki. Ya bayyana cewa, duk da muhimmancin sauye-sauyen da ake aiwatarwa domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, akwai wasu gidaje da al’ummomi da ka iya fuskantar matsaloli fiye da sauran jama’a. Saboda haka, ya ce akwai buƙatar samar da tsare-tsaren tallafi na musamman domin rage wa waɗannan mutane raɗaɗin sauye-sauyen.

Bagudu ya ce, annobar COVID-19 ta koyar da darasi mai muhimmanci kan yadda abubuwan da ba a yi tsammani ba za su iya rage kuɗaɗen shiga na gwamnati tare da raunana ƙarfin mutane da al’ummomi wajen tinkarar matsalolin tattalin arziki. Ya tuna cewa a lokacin annobar, raguwar kuɗaɗen shiga ta sa gwamnatoci suka fara duba yiwuwar rage kashe kuɗaɗe a wasu shirye-shiryen jin daɗin jama’a, ciki har da tallafin da ake bai wa masu ƙaramin ƙarfi.

A cewarsa, shirin NG-CARES ya samar da wata dama ta ƙarfafa ƙarfin gidaje da al’ummomi wajen farfaɗowa daga irin waɗannan matsaloli, maimakon a bar su su kaɗai su fuskanci illolinsu. Ministan ya ƙara da cewa muhimmancin shirin ya ta’allaka ne da yadda ba ya tsaya wa kawai ga bai wa mutane tallafi, domin yana bai wa al’ummomi damar gano matsalolin da suke fuskanta da kuma zaɓen irin matakan da suka dace domin magance su.

Ya bayyana cewa matsalolin da suka addabi wata al’umma na iya shafar sauran al’ummomi, don haka akwai buƙatar samar da tsare-tsaren ci gaba da za su ƙarfafa juriyar al’umma baki ɗaya wajen fuskantar ƙalubalen tattalin arziki. Saboda haka, Bagudu ya buƙaci jihohi 35 da ke cikin shirin da su yi cikakken amfani da damar da aka ba su, tare da tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen shirin yadda ya kamata domin inganta rayuwar al’ummominsu.

Haka kuma, ya ƙalubalanci jihohin da su ɗauki tallafin dala miliyan 500 da aka ware wa shirin a matsayin wata dama ta tabbatar da cewa ingantaccen aiwatar da shirye-shiryen tallafin jin daɗin jama’a da bunƙasa tattalin arziki na iya jawo ƙarin jarin kuɗi daga wasu masu zuba jari. A cewarsa, nasarar aiwatar da shirin za ta samar da hujjoji da za su ƙarfafa ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu, Bankin Duniya da sauran ƙungiyoyin haɗin gwiwar ci gaba, gami da kasuwannin hada-hadar jari, su ƙara tallafa wa irin waɗannan shirye-shirye.

By ukarofi

Leave a Reply