Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (wato NNPC) ya bayyana cewa, babban ɓangaren aikin bututun iskar gas na Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano (AKK) ya kusa kammaluwa, a daidai lokacin da wani kamfani ke neman a biya shi diyya kan filayen da aka ƙwace domin gudanar da aikin.
Kamfanin NNPC ya ce kammala aikin zai taimaka matuƙa wajen ƙara samun iskar gas, tare da bunƙasa samar da iskar gas ɗin da ake amfani da ita wajen tafiyar da motoci (CNG) a faɗin Arewacin Nijeriya.
Babban Daraktan Gudanarwa na Rukunin Kamfanonin NNPC, Bashir Ojulari, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a. A cewarsa, aikin bututun iskar gas na AKK ya kai kashi 95 cikin 100 na kammaluwa, inda sauran kashi biyar ɗin suka shafi kammala wasu cibiyoyin taimako da wuraren haɗa bututun da za su kai iskar gas ga masu amfani da ita.
Ya bayyana cewa faɗaɗa hanyoyin sadarwa na iskar gas zuwa wasu wurare zai ƙara samar da iskar gas ɗin CNG a yankin Arewa. Ojulari ya ce ana sa ran fara kai iskar gas zuwa Abuja kafin ƙarshen shekarar 2026 domin tallafa wa samar da wutar lantarki, masana’antu, cibiyoyin adana bayanai na kwamfuta da sauran manyan cibiyoyin kasuwanci.
Ya ƙara da cewa, ana sa ran Kaduna da Kano za su fara amfana da iskar gas ɗin nan da shekarar 2027. Ya kuma bayyana cewa NNPC ta yi nasarar tara jarin da ya kai dala biliyan 1.5 domin gudanar da aikin, bisa hasashen yawan iskar gas da za a iya jigilarwa ta cikin bututun. Ojulari ya ce, “An kammala babban bututun aikin iskar gas na AKK, wanda ya taso daga Ajaokuta ta Kaduna zuwa Kano. Ragowar kashi biyar cikin 100 ya shafi kammala wasu cibiyoyi da ake buƙata domin haɗa manyan bututun da za su kai iskar gas zuwa wuraren da masu amfani da ita suke.
“Muna fatan kafin ƙarshen wannan shekara za mu fara kai iskar gas zuwa Abuja a matsayin mataki na farko. Zuwa shekarar 2027 kuma, za mu faɗaɗa samar da iskar gas ɗin zuwa Kaduna da Kano. Sai dai yana da kyau a fahimci cewa wannan babban bututun ne kawai. Daga nan ne za mu gina ƙarin hanyoyin sadarwa zuwa wasu yankuna. Mun riga mun magance buƙatun matakin farko saboda a yanzu muna da tashar samar da wutar lantarki ta Abuja. Yayin da muka ƙara kutsawa zuwa arewacin ƙasar tare da kafa waɗannan hanyoyin sadarwa, samun iskar gas ɗin CNG zai ƙaru matuƙa. Har yanzu muna buƙatar faɗaɗa hanyar sadarwar zuwa Maiduguri da Sokoto. Saboda haka, akwai sauran ayyuka da za a gudanar. Amma yanzu aikin ya fi sauƙi fiye da jigilar iskar gas daga Fatakwal zuwa waɗannan wurare,” inji shi.
Ya bayyana cewa samar da wannan muhimmin tsarin sufuri na iskar gas zai sauƙaƙa hanyoyin rarraba ta zuwa sassa daban-daban na yankin Arewa. Bututun iskar gas na AKK yana da faɗin inci 40, kuma tsawonsa ya kai kilomita 614. Ya taso ne daga Ajaokuta da ke Jihar Kogi zuwa Kano, tare da wasu cibiyoyin sarrafawa da wuraren rarraba iskar gas da aka tsara domin jigilar iskar gas zuwa masana’antu da sauran manyan masu amfani da ita a Arewacin Nijeriya.
