Jihohi 14 kacal ke biyan fansho akan kari – PenCom

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Fansho ta ƙasa (PenCom) ta bayyana cewa jihohi 14 kacal ne daga cikin jihohin Nijeriya 36 ke biyan fansho a kai a kai, inda ta amince cewa wasu gwamnatocin jihohin na nuna gazawa wajen sauke nauyin da ke kansu na biyan haƙƙin ma’aikatan da suka yi ritaya.

Daraktar-Janar ta hukumar, Omolola Oloworaran, ce ta bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE NEWS a ranar Litinin. Ta ce biyan fansho na ci gaba da zama babban ƙalubale a wasu jihohi. Ta ce, “Jihohi 14 ne ke biyan fansho yadda ya kamata. Amma jihohi 14 cikin 36 adadi ne mai yawa. Wasu jihohin kuma suna yin mummunar sakaci.”

Sai dai Oloworaran ba ta bayyana sunayen jihohin 14 da ke biyan fansho a kai a kai ba, haka kuma ba ta ambaci jihohin da ke kasa cika wannan nauyi ba. Daraktar-Janar ɗin ta kuma bayyana cewa kuɗin Naira biliyan 400 da Gwamnatin Tarayya da ɓangaren harkokin fansho suka samar wa Asusun Kare Haƙƙin Masu Fansho (Pension Protection Fund), zai iya ɗaukar nauyin shirin tabbatar da mafi ƙarancin kuɗin fansho na wata-wata na tsawon aƙalla shekaru 10, bisa hasashen da aka yi a halin yanzu.

Ta ce, Gwamnatin Tarayya ta bayar da Naira biliyan 350, yayin da ɓangaren harkokin fansho ya bayar da Naira biliyan 50. Da take ƙarin bayani yayin hirar, Oloworaran ta ce hukumar ta ɗauki ƙwararren masani kan lissafin kuɗi da ƙididdigar haɗurra (Actuary) domin tantance yawan kuɗin da shirin zai buƙata da kuma hasashen ko za a iya ci gaba da gudanar da shi na dogon lokaci. Ta ce, “Idan muka yi hasashe bisa taka-tsantsan, kuɗin zai wadatar da mu na tsawon shekaru 10 masu zuwa. Ina nanatawa, bisa taka-tsantsan.”

Sai dai ta yi nuni da cewa za a iya sake duba wannan hasashe na kuɗaɗen bisa la’akari da hauhawar farashi da kuma adadin kuɗin da za a samu domin ci gaba da gudanar da shirin. Ta ce hukumar ta ƙuduri aniyar tabbatar da cewa masu karɓar fansho da ke cikin mawuyacin hali na ci gaba da samun tallafin kuɗi ta hanyar tsarin mafi ƙarancin fansho.

Oloworaran ta kuma bayyana cewa Asusun Kare Haƙƙin Masu Fansho yana da Naira biliyan 38 kafin gwamnatin da ke kan mulki ta kama aiki. Ta ƙara da cewa wani ɓangare na kuɗin da Gwamnatin Tarayya ta bayar an ware shi ne domin biyan bashin fansho da ya daɗe yana biye.

Ta ce kashi 54 cikin 100 na waɗanda suka amfana da kuɗaɗen shirin ya zuwa yanzu tsofaffin ma’aikatan kamfanoni ne masu zaman kansu, yayin da kusan kashi 70 cikin 100 na ma’aikatan da ake sa ran za su cancanci amfana da shirin su ma ke aiki a ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu.

Dangane da taƙaddamar da ta taso kan buƙatar wasu tsofaffin ’yan sanda na ficewa daga Tsarin Gudunmawar Kuɗin Fansho (Contributory Pension Scheme), su koma tsohon tsarin fansho mai ƙayyadadden adadin kuɗin da za a riƙa biya, Oloworaran ta ce hukumar na aiki tare da rundunar ’yan sanda domin samar da mafita da za ta kare kuɗaɗen fanshonsu. Ta bayyana cewa an gabatar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da zaɓuɓɓukan hanyoyin magance matsalar domin ya yi nazari a kansu. Ta ce babban abin da ake son tabbatarwa shi ne tsofaffin ’yan sandan sun samu ingantacciyar kulawa ta fuskar fansho.

By ukarofi

Leave a Reply