2027: INEC ta ƙara wa’adin ɗaukar aikin jami’an wucin-gadi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta sanar da ƙara wa’adin yin rajista ga masu ra’ayin yin aiki da ita na wucin-gadi (ad-hoc staff) domin zaɓukan 2027 da sati biyu, lamarin da ya bayar da damar kammala rajista ga masu yunƙurin neman aikin.

Hukumar ta ce, ta buɗe shafin neman aikin mai suna INEC Portal for Recruitment of Election Staff (INECPRES) a ranar 18 ga Satumba, 2026, wanda da fari an tsara rufewa a ranar 18 ga Nuwamba, 2026.

Saidai daga bisani bayan nazari kan aikin ɗaukar, INEC ta ƙara wa’adin rajistar zuwa ƙarfe 11:59 na dare a ranar Larabaw, 3 ga Disamba, 2026.

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe (IVEC), Mohammed Kudu Haruna ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a, 20 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce an ɗauki matakin ne da nufin bai wa ‘yan Nijeriya da suka cancanta damar neman aikin da tabbatar da hukumar ta samu wadataccen adadin mutanen da take buƙata a faɗin Nijeriya.

Akan haka sanarwar ta kirayi ‘yan Nijeriya da suka cancanta da su miƙa bayanan neman aikin ta sahihin shafin ta na https://pres.inecnigeria.org kafin sabon wa’adin ya ƙare.

Ta kuma tunatar da masu nema cewa baki ɗaya hanyoyin neman aikin kyauta ne, tana mai gargaɗin cewa babu wani jami’in INEC ko wani mutum da aka sahale wa karɓar kuɗi daga hannun masu neman aikin. Sannan, ta yi kira a gare su da su ƙaurace wa shafukan ‘yan damfara da dukkan wani saƙon kar-ta-kwana da ke tayin samun aikin a wajen shafin.

By Babaji

Leave a Reply