Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsawon fiye da shekaru goma, ’yan Nijeriya sun san mace guda ɗaya ce kawai a matsayin matar tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wato uwargidansa, Dame Patience Jonathan, wadda ta shahara da fito-na-fito da bayyana ra’ayoyinta. Sai dai yanzu wannan fahimta ta fara sauyawa, bayan wata mata mai suna Dakta Ayima Lott-Jonathan, wadda aka daɗe ana yaɗa labarin cewa ita ce matar Jonathan ta biyu, ta shirya fitowa fili domin bayyana tarihin rayuwarta ta hanyar wallafa wani littafi. Littafin nata mai suna Gold Dust: Treasures of ƙuiet Years (Wuraren Taska a Shekarun Shiru), zai zama hanyar da za ta bayyana abubuwan da suka faru a rayuwarta tsawon shekarun da ta shafe ba tare da kasancewa cikin idon jama’a ba.
Taken littafin ya yi nuni da irin rayuwar da ta shafe tana yi a ɓoye. A lokacin da Patience Jonathan ke riƙe da muƙamin Uwargidan Shugaban ƙasa a Fadar Aso Rock, Ayima Lott-Jonathan na nan, tana gudanar da rayuwarta ba tare da yawan fitowa a bainar jama’a ba.
A ranar 19 ga Nuwamba, 2026, wadda za ta cika shekaru 50 da haihuwa, Dakta Ayima za ta ƙaddamar da littafin tare da bayyana nata labarin a karon farko ga jama’a. Za a gudanar da bikin ne a Makarantar ƙasa da ƙasa ta Aduvie da ke Jahi, Abuja. Makarantar, wadda ita ce ta kafa a shekarar 2008, tana cikin yankin Maitama, inda ta gina gagarumar cibiyar ilimi ba tare da dogaro da hasken siyasa ko fitowar jama’a ba.
Jerin manyan baƙin da ake sa ran za su halarci bikin ya nuna cewa ba wani ƙaramin taron iyali ba ne, domin an gayyaci manyan jiga-jigan siyasa da sarakunan gargajiya.
Daga cikin waɗanda aka gayyata akwai:
Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Goodluck Jonathan, wanda zai halarta a matsayin Babban Baƙo na Musamman. Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Namadi Sambo, wanda zai jagoranci taron. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda zai gabatar da littafin ga jama’a. Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, da takwaransa na Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, waɗanda za su kasance masu masaukin baƙi a taron.
Sarkin gargajiya King Bubaraye Dakolo Agada IV, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta Jihar Bayelsa, zai kasance uban taron na musamman.
Shirya irin wannan jerin manyan baƙi ya nuna irin girman taron da kuma muhimmancin da aka bai wa fitowar marubuciyar fili, duk da cewa a baya ba a gabatar da ita a hukumance ga al’ummar Nijeriya a matsayin wata mace mai alaƙa da tsohon shugaban ƙasar ba.
Littafin, wanda ya ƙunshi babi 12, zai samu sharhin Farfesa G.G. Darah, wanda yake cikin ƙwararrun masana da ke da muƙamin zama ɗan ƙungiyar masana adabin Nijeriya (Fellow of the Nigerian Academy of Letters).
Littafin ba wai tarihin rayuwa kawai zai ƙunsa ba, a cewar rahoton, domin zai bayyana muhimman matakan da ta bi a rayuwarta, tun daga karatun lauya a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas, har zuwa lokacin da aka kira ta cikin sahun lauyoyi a shekarar 2003.
Ita ’yar tsohon Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Bayelsa ce, Cif F.D. Lott. Haka kuma, ’yar uwan tsohuwar Ministar Man Fetur ta Nijeriya, Diezani Alison-Madueke, ce.
