Gwamnatin Tarayya ta fara gina sabuwar masana’antar samar da fasfon intanet mafi girma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce ta fara aikin gina katafariyar masana’antar samar da fasfon intanet (e-passport) a hedikwatar Hukumar Shige-da-Fice ta Ƙasa (NIS) da ke Abuja. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo tare da Sanata Adams Oshiomhole da wasu ne suka dasa fandishon aikin a ranar Juma’a Abuja, yayin bikin dude babban aikin.

Tunji-Ojo ya ce, aikin, wanda ake sa ran kammalawa a watan Mayun 2027, zai samar da yanayin haɗa takardun fasfon Nijeriya, rage dogaro da samarwa daga waje da bayar da kariya daga matsalolin da ake fuskanta yayin shigo da su daga ƙasashen waje zuwa Nijeriya. Ya bayyana aikin a matsayin gagarumar nasara a NIS ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewarsa, aikin zai lanƙwame faɗin fili da ya kai hekta 1.1, wanda za a yi amfani da fasahar zamani wajen gudanar da ayyukansa ta yadda za a iya ganin ko’ina a faɗin duniya daga harkokinta.

Kazalika, ya ce masana’antar za ta riƙa samar da jimillar takardun fasfo guda miliyan shida zuwa goma a nan da watan Mayu da zarar an buɗe ta. Nijeriya na buƙatar guda miliyan 1.8 zuwa miliyan 2. Wannan na nufin masana’antar za ta amfanar da ƙasashen Afirka da dama da suke siye daga ƙasashen Turai da Amurka.

By Babaji

Leave a Reply