
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ‘Yan jarida ta Ƙasa (NUJ) reshen Abuja, ta sanar da jimaminta ga rasuwar tsohon Shugabanta, Mista Abdul Jelil Adebayo.
An haifi Adebayo ne a ranar 23 ga Maris na shekarar 1964 a Ƙaramar Hukumar Abeokuta ta Arewa a Jihar Ogun, wanda ya rasu bayan shafe shekaru 62 a duniya.
A matsayinsa na shugaban ƙungiyar, Adebayo ya hidimta mata bisa jajircewa, sadaukarwa da ƙwarewa, lamarin da ya taimaka wajen bunƙasa walwalar ‘yan jarida da ci-gaban fannin.
Jagorancin nasa, hikima da tawali’unsa sun taimaka masa wajen samun girmamawa daga abokan aiki a Abuja da wajenta. Rashin sa ya haifar da babban giɓi ga NUJ FCT, aikin jarida da makusantansa.
Ƙungiyar a madadin dukkan mambobinta, ta miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan marigayin, abokan aiki da abokan arziƙi, tana mai fatan Ubangiji ya masa rahama tare da bai wa makusanta haƙurin juriyan rashin sa.
