Majalisar Arewarmu Duniyarmu ta naɗa Madingo Garkuwan Afirka

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Majalisar Masarautar Arewarmu Duniyarmu African Chiefdom and Council ta naɗa wasu fitattun mutane daga ƙasashen Afirka sarautun gargajiya daban-daban, a wani mataki na ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin nahiyar.

Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Uboya Dr Yussif Iddrisu Madingo, wanda aka ba sarautar Garkuwan Afirka (Kowa Naaso) bisa la’akari da gudunmawarsa wajen haɗa kan al’umma da bunƙasa zaman lafiya.

An gudanar da bikin naɗin sarautun ne a Abuja, inda aka naɗa wasu fitattun mutane sarautu daban-daban, waɗanda suka haɗa da Sheikh Ismail Abubakri Bamaiyi, Sarkin Malamai na Afirka; Dr Surajo AbdulKarim Kwami, Sarkin Lafiyar Arewa; da Ambasada Alhaji Ibrahim Babalili Abdullahi (Jarman African), Sarkin Hausawan Kano na Arewarmu Duniyarmu African Chiefdom and Council.

Da yake jawabi a wajen bikin, shugaban majalisar masarautar, Mai Martaba Ambasada Alhaji Ibrahim Haruna, ya ce an zaɓi waɗanda aka naɗa ne bisa la’akari da kishin al’umma, jajircewa da gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta zaman lafiya da haɗin kai.

Ya bayyana cewa manufar naɗin sarautun ita ce samar da wata dama ta haɗa ƙarfi da tunani tsakanin sarakunan gargajiya, malamai, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki domin gina Afirka mai haɗin kai da ci gaba.

A cewarsa, sarautun da aka bayar ba wai don ado ko ɗaukaka sunayen waɗanda aka naɗa ba ne, illa dai wata amana ce da ta ɗora musu nauyin yi wa al’umma hidima.

“Daga yau, wannan sarauta ba ado ba ce kawai, babban amana ce da nauyi a wuyansu. Muna son su zama jakadun alheri, zaman lafiya da haɗin kai a duk inda suke a nahiyar Afirka,” in ji shi.

Ambasada Haruna ya buƙaci sabbin masu sarautun da su yi amfani da matsayinsu wajen sasanta rikice-rikice, ƙarfafa zumunci, taimaka wa marasa ƙarfi da kuma kare martabar al’adu da addinan al’ummomin Afirka.

Ya jaddada cewa majalisar ba ta bayar da sarautun ne domin fifita wata ƙabila ko ƙasa a kan wata ba, sai dai don samar da haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummomin nahiyar.

Ya ce babban darajar sarauta ba ta ta’allaka ga rawani ko kujerar mulki kawai ba, tana kuma cikin adalci, tausayi, gaskiya, tawali’u da jajircewa wajen yi wa jama’a hidima.

A nasa jawabin godiya bayan karɓar sarautar Garkuwan Afirka, Uboya Dr Yussif Iddrisu Madingo (Kowa Naaso) ya bayyana farin cikinsa da godiya bisa wannan karramawa da majalisar ta yi masa.

Ya yi alƙawarin yin amfani da sabon matsayinsa wajen ƙara haɗa kan al’umma, inganta fahimtar juna da samar da daidaito da zaman lafiya a tsakanin al’ummomi.

Madingo ya kuma bayyana cewa zai yi ƙoƙarin tabbatar da cewa amana da nauyin da aka ɗora masa sun zama sanadin ƙarfafa zumunci da haɗin kai, ba tare da nuna bambanci tsakanin ƙabila, addini ko ƙasa ba.

By ukarofi

Leave a Reply