
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi suka ga jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), wadda a ƙarƙashinta ne Gwamna Seyi Makinde yake takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, inda ya bayyana mambobinta a matsayin waɗanda ba su da wajen zuwa.
Tinubu ya bayyana haka ne Ibadan a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Babban Birnin Jihar Oyon. Saidai bai kira jam’iyyar da gwamnan ba da sunayensu. Ya ce, “Mun ji cewa akwai wata ƙungiya/tsagi da ake kira da ƙungiyar ‘Palemo’ (tarkace). Kada ku damu da su; suna jiran rashin tsammani ne kaɗai; ba su da wajen zuwa.”
Kalaman, waɗanda aka yi su a mahaifar Gwamnan na Oyo, ana ganin ya yi su ne akan jam’iyyar APM, wadda Makinde ne ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Da fari Makinde ya ayyana ƙudirinsa na tsaya wa takara a ƙarƙashin APM luma daga bisani aka ba shi tikitin a jam’iyyar, inda ya ce alwashin daidaita al’amuran Nijeriya.
Shugaba Bola Tinubu da farko ya umarci a gi gangamin ba tare da jama’a masu yawa ba don karrama waɗanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a ranar Juma’a a yankin Ukubie da ke Ƙaramar Hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa.
