An yi wa jaruma Kareena Kapoor kashedi kan sarka mai dauke da ƙur’ani da ta sanya

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Fitacciyar jarumar fina-finan Indiya, Kareena Kapoor Khan, ta tsinci kanta a cikin takaddama bayan sanya wata sarƙa mai ɗauke da rubutun Ayatul Kursiyyu, lamarin da ya sa aka aika mata da takardar sanarwar shari’a tare da neman ta cire hotunan da ta wallafa da ke nuna kayan adon.

Takaddamar ta samo asali ne daga wasu hotunan da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram yayin bikin Diwali, inda ta bayyana cikin wata doguwar riga mai launin toka mai haske, tare da rawani mai launi iri ɗaya da kuma wata sarƙa mai ɗauke da babban dutse mai daraja.

Abin da ya fi ɗaukar hankali a cikin kayan adon shi ne rubutun Ayatul Kursiyyu da ke jikinsa, wadda ita ce aya ta 255 a cikin Suratul Baƙara. An bayyana cewa sarƙar tana ɗauke da wani dutse mai daraja na Emerald mai nauyin carat 30, wanda aka sassaka rubutun ayar a jikinsa.

Rahotanni sun nuna cewa wannan sarƙa ba sabon kayan ado ba ne da aka ƙera domin Kareena, domin ana danganta ta da tarihin gidan sarautar Bhopal, inda ta kasance cikin kayan adon da ake gadon mallakarsu a iyalan gidan sarautar.

Mai tsara wa Kareena sutura, Rhea Kapoor, ita ce ta bayyana tarihin kayan adon a cikin wani saƙo da ta wallafa, inda ta ce sarƙar ta kasance mallakar Begum ta Bhopal, kuma ta shigo hannun Kareena ne ta hanyar dangin mijinta, Saif Ali Khan.

A cewarta, kakar Saif, Sajida Sultan, ita ce ‘yar tsohon sarkin Bhopal, Hamidullah Khan, kuma kayan adon sun kasance cikin abubuwan tarihi da iyalin suka gada daga kakanninsu.

Sai dai sanya sarƙar a cikin hotunan bikin Diwali ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman bayan Abbas Hafeez, wani jagoran jam’iyyar Congress a Indiya, ya aika wa Kareena da Rhea Kapoor takardar sanarwar shari’a mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2026.

A cikin takardar, ya nuna rashin amincewarsa da yadda aka nuna kayan adon mai ɗauke da ayar Alƙur’ani, yana mai cewa ya kamata a kula da irin yadda ake gabatar da wani abu mai ɗauke da rubutun Alƙur’ani mai girma domin a kiyaye martabarsa.

Ya kuma buƙaci a cire hotuna da bidiyoyin da ke nuna sarƙar daga shafukan sada zumunta, tare da neman Kareena da mai tsara mata suturar su bayar da haƙuri a bainar jama’a.

Sai dai abin lura shi ne cewa ƙorafin bai shafi ‘yancin Kareena na sanya sutura ko kayan ado gaba ɗaya ba, a’a, ya ta’allaka ne kan yadda aka gabatar da wani abu mai ɗauke da ayar Alƙur’ani a matsayin kayan ƙawata jiki.

Lamarin ya sake buɗe tattaunawa kan yadda ya kamata a riƙa kula da abubuwan da suke da alaƙa da addini, musamman idan aka mayar da su cikin kayan ado da ake amfani da su a bukukuwa da shagulgulan nishaɗi.

Kareena Kapoor dai tana daga cikin fitattun jaruman Bollywood da suka shafe shekaru suna taka rawa a masana’antar fina-finan Indiya, yayin da aurenta da Saif Ali Khan ya kuma sanya ta kasance cikin iyalan tsohuwar sarautar Bhopal.

By ukarofi

Leave a Reply