ASCSN ta nemi Gwamnatin Tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 300,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnatin Nijeriya (ASCSN), ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata zuwa Naira 300,000 a kowane wata, tana mai cewa albashin Naira 70,000 da ake biya a halin yanzu bai isa ya ba ma’aikata damar gudanar da rayuwa cikin walwala ba, sakamakon tsadar kayayyaki da taɓarɓarewar tattalin arziki.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Shehu Mohammed, ne ya gabatar da wannan buƙata yayin taron Majalisar Zartarwa ta ƙasa (NEC) ta ƙungiyar da aka gudanar a Abuja, wanda Ministan ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Dakta Muhammadu Maigari Dingyadi, ya halarta.

Mohammed ya bayyana cewa hauhawar farashin kayan abinci, sufuri, makamashi da kuɗaɗen kula da lafiya sun ƙara jefa ma’aikata cikin mawuyacin hali, inda albashin da suke karɓa ya kasa biyan muhimman buƙatun yau da kullum.

Ya ce halin da ake ciki ya nuna cewa akwai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta sake duba tsarin albashin ma’aikata cikin gaggawa, domin tabbatar da cewa abin da suke samu ya dace da tsadar rayuwa da kuma nauyin da ke kansu.

Shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa bai kamata gwamnati ta dogara da tallafin wucin gadi ko ƙarin kuɗaɗen agaji ga ma’aikata domin magance matsalar ƙarancin albashi ba, yana mai cewa irin waɗannan matakai ba za su iya samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin tattalin arzikin da ma’aikata ke fuskanta ba.

A cewarsa, ƙungiyar na ganin cewa ya kamata gwamnati ta ɗauki matakin ƙara albashin ma’aikata kai tsaye, maimakon ci gaba da samar da tallafe-tallafe waɗanda ba su da tabbacin ɗorewa.

Mohammed ya kuma yi nuni da cewa rashin cikakken aiwatar da wasu yarjejeniyoyin tallafin kuɗi da aka amince da su a shekarar 2023 ya raunana amincewar ma’aikata ga irin waɗannan shirye-shirye.

Ya ce maimakon gwamnati ta jira lokacin sake tattauna sabon mafi ƙarancin albashi kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, ya kamata ta ɗauki matakin gaggawa na ƙara albashin ma’aikacin da yake kan matakin mafi ƙanƙanta zuwa Naira 300,000 a kowane wata.

Ya ƙara da cewa, duk wani ƙarin albashi da za a amince da shi ya kamata ya shafi sauran matakan albashin ma’aikatan gwamnati, domin kada a samu rashin daidaito tsakanin ma’aikatan da ke matakai daban-daban na aiki.

A cewarsa, ƙarin albashin zai taimaka wajen farfaɗo da ƙarfin sayen ma’aikata, tare da ba su damar biyan buƙatun iyalansu da sauran nauyin da ke kansu.

A nasa ɓangaren, Ministan ƙwadago da Samar da Ayyukan Yi, Dakta Muhammadu Maigari Dingyadi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago da su ƙarfafa haɗin gwiwa da tattaunawa domin warware matsalolin da suka shafi jin daɗin ma’aikata.

Ministan ya bayyana cewa ya kamata a riƙa warware saɓanin da ke tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago ta hanyar tattaunawa mai ma’ana, maimakon dogaro da yajin aiki ko tsawaita taƙaddama.

Dingyadi ya yi wannan jawabi ne a taron da aka gudanar ƙarƙashin taken Daga Saɓani zuwa Haɗin Kai (From Confrontation to Collaboration), inda ya jaddada muhimmancin fahimtar juna tsakanin ɓangarorin biyu wajen samar da ingantacciyar dangantaka a fannin ƙwadago.

Ya ce haɗin kai tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin ma’aikata zai taimaka wajen samar da mafita ga matsalolin da ma’aikata ke fuskanta, tare da tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a hukumomin gwamnati.

Buƙatar ƙungiyar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tasirin tsadar rayuwa ga ma’aikatan Nijeriya, musamman ganin cewa mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 da ake amfani da shi a halin yanzu ya fara rasa ƙimar sayensa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da hidimomi.

Sai dai, buƙatar ƙarin albashin zuwa Naira 300,000 matsaya ce da ƙungiyar ta gabatar, ba wai sabon mafi ƙarancin albashi ne da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi ba.

By ukarofi

Leave a Reply