Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata ƙungiyar agaji mai zaman kanta, Mumsbooth Empowerment Initiative, ta horas da mata matasa 142 kan yadda za su taka rawa a harkokin shugabanci, shiga cikin al’amuran mulki da kuma bayar da shawarwari kan manufofin gwamnati, a wani yunƙuri na ƙarfafa rawar da mata ke takawa wajen yanke shawarar da ta shafi rayuwar al’umma.
An gudanar da horaswar ne ƙarƙashin wani shiri mai taken Her Voice, Her Rights: Inclusive Civic and Policy Action Hub, wato wani dandali da aka samar domin ƙarfafa muryoyin mata, kare haƙƙoƙinsu da kuma ba su damar shiga harkokin shugabanci da tsara manufofin da suka shafi al’ummominsu. Shirin ya samu goyon bayan Asusun Samar da Makomar Matasa na Nijeriya, wato Nigeria Youth Futures Fund.
Taron ya gudana ne a Treasure Island Abuja Zoological Park, Babban Birnin Tarayya.
Wanda ta kafa ƙungiyar Mumsbooth Empowerment Initiative, Martha Tawiyah, ta bayyana cewa manufar shirin ita ce bai wa mata matasa ilimi, ƙwarewa da ƙarfin gwiwar da za su taimaka musu wajen taka rawar gani a harkokin mulki, tare da samun damar yin tasiri ga manufofin da ake samarwa domin tafiyar da al’ummominsu.
A cewarta, shirin zai taimaka wajen fahimtar muhimmancin kasancewar mata cikin tsarin yanke shawara, musamman a matakan da suka shafi ci gaban al’umma da tsara manufofin gwamnati.
Tawiyah ta ce, an samu halartar mata 142 daga cikin kusan 200 da suka yi rajistar neman shiga shirin, lamarin da ta ce ya nuna yadda sha’awar mata matasa ke ƙaruwa wajen shiga harkokin farar hula da fahimtar yadda ake tsara manufofin gwamnati.
Ta bayyana cewa ƙarfafa mata su fahimci haƙƙoƙinsu da nauyin da ke kansu a cikin al’umma zai taimaka wajen samar da shugabanci mai inganci da kuma tabbatar da cewa ba a ware ra’ayoyinsu a lokacin yanke muhimman shawarwari ba.
Shirin ya kuma mayar da hankali kan muhimmancin bai wa mata damar bayyana ra’ayoyinsu, shiga tattaunawar da ta shafi manufofin gwamnati da kuma fahimtar hanyoyin da za su bi domin isar da buƙatunsu ga hukumomin da abin ya shafa.
Wani muhimmin ɓangare na shirin shi ne tabbatar da cewa mata masu buƙata ta musamman ma sun samu damar shiga harkokin shugabanci da yanke shawara, ba tare da fuskantar wariya ko wani nau’in tauye haƙƙi ba.
Wannan yunƙuri na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara jaddada muhimmancin shigar mata cikin harkokin shugabanci da samar da manufofin da za su amfanar da dukkan ɓangarorin al’umma.
Masana harkokin ci gaban al’umma sun sha bayyana cewa, rashin samun wakilcin mata a wuraren yanke shawara na iya sa a yi watsi da wasu buƙatu da matsalolin da suka shafe su kai tsaye.
Saboda haka, horas da mata kan jagoranci, haƙƙoƙin jama’a da yadda ake tsara manufofi na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen ƙara yawan matan da ke taka rawa a harkokin mulki da ci gaban ƙasa.
Kungiyar Mumsbooth Empowerment Initiative ta bayyana cewa tana son ƙarfafa mata ta hanyar ilimi da samar musu da damarmaki, domin su zama masu bayar da gudummawa wajen sauya rayuwarsu da kuma inganta al’ummomin da suke zaune.
