Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ƙaramar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara tana cigaba da samun koma baya, yayin da wasu manyan ‘ya’yanta guda uku suka fice daga jam’iyyar.
Waɗanda suka yi murabus din sune Hon. Shehu Muhammed Faru, tsohon Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Hon. Moyi Aliyu Abbas, Sardaunan Magami, da Hon. Ishaka Abubakar (Dan Ila Mai Lemu) Gora.
A cikin takardar murabus mai ɗauke da ranar 6 ga Oktoba, 2026, mutanen uku sun sanar da matakin su na ficewa daga jam’iyyar APC nan take.
A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa a harkar yaɗa labarai, Comrade Halliru Attahiru Kakin Dawa ya sanya wa hannu, sun ɗauki matakin ne saboda abin da suka bayyana a matsayin rashin shugabanci na ƙwarai da halin ko in kula da jam’iyyar APC ke nuna wa magoya bayanta na ƙwarai.
“Wannan mataki ya samo asali ne sakamakon rashin shugabanci na gari, da kuma halin ko-in-kula da jam’iyyar APC ke nuna wa magoya bayanta,” inji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana murabus ɗin a matsayin babban rashi ga jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Maradun, idan aka yi la’akari da ƙarfin siyasar waɗanda suka fice da kuma yawan magoya bayansu a matakin ƙasa.
Hon. Faru, tsohon shugaban ƙaramar hukuma, na ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar a yankin, yayin da sauran biyun suma aka san su da yawan magoya baya a mazaɓunsu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ba a dai san jam’iyyar da ‘yan siyasar uku za su koma ba, amma majiyoyi na kusa da su sun bayyana cewa suna ci gaba da tuntuɓa da wasu jam’iyyun siyasa.


