Daga AISHA ASAS
Gidan Big Brother Naija Season 11 ya gamu da wani sabon sauyi bayan ɗaya daga cikin masu takarar shirin, Neche, ta yanke shawarar ficewa daga gasar da kanta.
Masu shirya shirin sun bayyana cewa Neche ta ɗauki matakin ne saboda wasu matsalolin kanta da suka buƙaci kulawarta, lamarin da ya sanya ta bar gidan ba tare da an fitar da ita ta hanyar ƙuri’ar masu kallo ba.
Neche ta sanar da ficewarta ne a ranar Lahadi, 16 ga Agusta, abin da ya ba sauran ‘yan gidan mamaki, musamman ganin cewa a lokacin tana riƙe da mukamin Head of House. Rahotanni sun bayyana cewa ficewar tata ta zo ne kwatsam, yayin da masu kallo ke ci gaba da bibiyar yadda take tafiyar da makonni na farko na gasar.
Masu shirya shirin sun ce dalilin ficewar yana da alaka da wasu muhimman al’amura na kanta, amma ba su bayyana cikakken bayani kan abin da ya faru ba. Hakan ya sa labarin ficewarta ya jawo tambayoyi daga masu kallon shirin da ke son sanin abin da ya sa ta yanke wannan shawarar.
Ficewar Neche ta kuma zama ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a wannan kakar ta BBNaija, wadda tuni ta fara samun cece-kuce da tattaunawa mai yawa a kafafen sada zumunta.
