Harin Rasha ya kashe mutane 10 a Ukraine yayin da Kiev ta kai hari kan Moscow

Spread the love

Akalla mutane 10 sun mutu a wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai wani ƙauye a yankin Kharkiv na Ukraine, yayin da Ukraine ita ma ta kai ɗaya daga cikin hare-haren jirage marasa matuka mafi girma kan Rasha tun bayan fara yakin.

Harin na Rasha ya afkawa kauyen Pechenihy ne a ranar Talata, inda mutane 10 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 17 suka jikkata. Shugaban yankin Kharkiv ya ce fararen hula ne harin ya rutsa da su.

A gefe guda kuma, Ukraine ta aika da kusan jirage marasa matuka 800 zuwa yankunan Rasha, ciki har da Moscow da wasu yankunan da ke ƙarƙashin ikon Moscow. Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce ta kakkaɓo jirage 791, yayin da wasu suka haddasa ɓarna da raunuka.

Sabon musayar hare-haren na zuwa ne yayin da yakin ya shiga wani sabon yanayi, inda Ukraine ke ƙara amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare mai nisa cikin ƙasar Rasha, yayin da Moscow ke ci gaba da kai hare-hare kan birane da kauyukan Ukraine.

By ukarofi

Leave a Reply