Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da kasuwanci da Iran

Spread the love

Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da dukkan harkokin kasuwanci da mu’amalar kuɗi da Iran har sai wani sabon sanarwa, matakin da ya ƙara tsananta rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Sanarwar ta zo ne bayan UAE ta ce ta gano makamai masu linzami guda biyu da aka harba daga Iran, waɗanda ta yi zargin cewa an nufi zirga-zirgar jiragen ruwa da su. Kasar ta ce makaman sun fada cikin teku, amma ta dauki matakin dakatar da harkokin kasuwanci saboda abin da ta kira ƙara tabarbarewar tsaron yankin. 

Iran ta musanta zargin, inda kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Esmaeil Baghaei, ya bayyana ikirarin UAE a matsayin maras tushe. 

Matakin na UAE ya zo ne a lokacin da rikicin Iran da Amurka ke kara yin tasiri a ƙasashen Gulf, musamman bayan rashin tabbas kan makomar mashigar Hormuz. ƙasashen biyu dai sun dan rage takun-saka a baya, amma sabon rikicin na iya sake kawo cikas ga alaƙar kasuwanci da diplomasiyya tsakaninsu.

By ukarofi

Leave a Reply